Me ya sa kasashen duniya ke korar jami'an diflomasiyyar Rasha?

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta sha alwashin mayar da kakkausan martani kan matakin da kasashe fiye da 20 suka dauka na korar jami'an diflomasiyyarta domin mayar da martani ga sanya guba da aka yi wa wani tsohon jami'in leken asirin Rashan a Birtaniya.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ware Amurka kadai daga cikin kasashen don yin ramuwa bayan da ta kori jami'an diflomasiyyarta 60 ta kuma rufe ofishin jakadancinta.
Amma mataimakin ministan harkokin waje Sergei Ryabkov, ya ce Rasha ba za ta watsar da tattaunawar zaman lafiya da ta fara da Amurka ba.
Ana ganin korar jami'an leken asirin Rasha 100 da aka yi a matsayin mafi girma da ya taba faruwa a tarihi.
Wannan yana daga cikin gagarumin mayar da martanin da aka shirya kan Rasha, bayan da aka kai wa wani tsohon jami'in leken asirin kasar Sergei Skripal da 'yarsa Yulia, harin gubar nerve a Birtaniya a farkon watan nan.
A makon da ya gabata ne shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya suka amince cewa Rasha ce ta kai wa Mista Skripal wannan hari.
Wanne martani Rasha ta mayar?
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta kira wannan gagarumar kora da cewa "rashin kyakkyawar mu'amala" ce ta kuma ce za ta yi wani abu kan hakan.
Ma'aikatar ta ce za ta tsara jerin matakan mayar da martani a gabatar wa Shugaba Putin don neman amincewarsa.

An ambato wani dan majalisar dattawan Rasha Vladimir Dzhabarov, yana cewa "dole a yi ramuwar gayya" ga matakin na Amurka na korar jami'an diflomasiyyar Rasha 48 da ke birnin Washington, da kuma 12 da ke wakiltar kasar a Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York.
Ofishin Jakadancin Rasha da ke Amurka ya wallafa martaninsa a shafinsa na Twitter kan rufe ofishin jakadancin da ke birnin Seattle.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Mr Ryabkov ya ce ana bukatar daukar kwararan matakai kan abun da Amurka ta yi, amma ya jaddada cewa Rasha ba za ta watsar da tattaunawar zaman lafiya da ta fara da Amurka ba, wanda aka fara a baya-bayan nan tsakanin Shugaba Putin da Shugaba Trump ta wayar tarho, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti ya ruwaito.

Wa ye yake korar jami'an diflomasiyya?
A farkon watan nan ne Birtaniya ta sanar da korar jami'an diflomasiyyar Rasha 23.
Wasu kasashen da dama su ma sun sanar da cewa suna daukar irin wannan mataki don nuna goyon baya a ranar Litinin. Kasashen sun hada da:
- Amurka: Jami'an diflomasiyya 60
- Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai: Faransa (4); Jamus (4); Poland (4); Jamhuriyyar Czech (3); Lithuaniya (3); Denmark (2); Netherlands (2); Italiya (2); Sipaniya (2); Estoniya (1); Croatiya (1); Finland (1); Hungary (1); Latviya (1); Romaniya (1); Sweden (1)
- Ukraine: 13
- Canada: 4, da kuma kin amincewa da bukatar Rasha na wasu karin jami'an uku da ta nema
- Albania: 2
- Australiya: 2
- Norway: 1
- Macedoniya: 1
Kasar Iceland ma ta sanar da dakatar da wani taron koli na tattaunawa da hukumomin Rasha, kuma shugabanninta sun ce ba za su halarci Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara a Rashan ba a watan Yuni.
A farkon watan nan ne Birtaniya ta ce ba za ta tura ministoci da mambobin gidan sarautar kasar Gasar Cin Kofin Duniyar ba.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson, ya yaba wa kawayen Birtaniyar kan hadin kan da suka nuna wajen mayar da martani irin wanda kasarsa ta dauka.
A wata hira da ya yi da BBC ya ce "Dole Rasha ta sauya halayyarta don duniya ta gaji da irin wannan hali nata," amma kuma ya yi watsi da batun cewa ana dulmiya cikin fadan cacar baka, kuma ya jaddada cewa Burtaniya ba ta da matsala da jama'ar Rasha.
Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da suka ce ba su da aniyar korar jami'an diflomasiya sun hada da Austriya da Girka da Portugal, ko da yake sun ce suna goyon bayan Birtaniya kuma sun yi Allah-wadai da gurbar sa aka sanya wa tsohon jami'in leken asirin Rasha.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Fira ministar New Zealand Jacinda Arden, ta ce ba su da jami'an leken asirin Rasha a kasarsu, amma ta ce idan suna da su to ko shaka ba bu za su koresu.
Shin me yasa suka dauki wannan mataki?
A ranar Litinin ne Australiya ta bi sahun sauran kasashe duniya irin su Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai wajan shelar cewa za ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Rasha biyu da ake zargin cewa su jami'an leken asirin ne da ba a bayyanasu ba.
Firai Minista Malcolm Turnbull ya yi misali da kutsen da aka yi a zabe da kuma barazana da ake yi wa abokansu, kuma ya ce "harin da aka kai a Saliisbury hari ne da aka kai wa dukkaninmu".
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya ce kasashen Turai sun yanke shawarar korar jami'an diflomasiyyar Rasha ne sakamakon taron da suka yi a makon da ya gabata game da harin gubar da aka kai a Salisbury.
"Karin matakai sun hada da karin korar da za a yi a kasashen Turai a cikin kwanaki da kuma makwanni masu zuwa", a cewarsa.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka a cikin wata sanarwa ta ce "a ranar 4 ga watan Maris, Rasha ta yi amfani da wata guba da ke yin illa ga lakar bil'adama domin kokarin kashe wani dan dan Birtaniya da kuma 'yarsa da ke Salisbury."
Wannan hari da aka kai wa abokiyarmu Birtaniya ya jefa rayuwar mutanen da ba su ji ba su gani ba cikin hadari, kuma ya raunata mutane uku ciki har da jami'in dan sanda.
Ta bayyana harin a matsayin tamkar keta hakkin yarjejeniyar kawar da makamai masu guba ne kuma abu ne da ya sabawa dokokin kasashen duniya."

Nuna goyon baya da baa taba ganin irinsa ba a tarihi
SharhinJonathan Marcus, wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya
Wannan na son ya koma rikicin diflomasiyya mafi girma da ake yi tsakanin Rasha da kuma kasashen yamma tun bayan da Rasha ta kwace yankin Crimea.
Sai dai duk da cewa Rasha ta musanta yin haka, kawayen Birtaniya sun amince da matsayinta akan cewa an yi amfani da guba da ke yin illa ga lakar jikin bil'adama a Salisbury kuma watakila Rasha na da hannu a ciki.
Korar da Amurka da kasashen Turai suka yi, nuna goyon baya ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi kuma yana zuwa ne a dai dai lokacin da dangantaka tsakanin Birtaniya da kasashen Turai ke kara tsami, sakamakon tattaunawar da suke yi game da ficewarta daga Tarayyar Turai.
Bayanin da shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya yi akan cewa za a dauki karin matakai, wata alama ce ga Rasha yayin da suke nazari akan matakin da za su dauka domin mayar da martani.
Wannan babbar nasara ce ta fuskar diflomasiya ga Firai Ministar Burtaniya Theresa May - kuma bayan matakin mai karfi da aka dauka kawayen Burtaniya sun kuma nuna goyon baya mai karfi.
Haka kuma wannan ya sa gwamnatin Shugaba Trump ta tsaurara matsayinta akan Rasha.













