Mutum 32 sun mutu a hatsarin jirgi a Rasha

An-26. File photo

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Wani jirgi mallakin wani kamfanin kasar Rasha ya yi hatsari a yayin da yake sauka a sansanin soji na Hmeimim a Syria, a cewar rundunar sojin Rasaha.

Dukkan fasinjoji 26 da jke cikin jirgin sun mutu da kuma ma'aiakatan cikin jirgin shida, a cewar ma'aiakatar tsaron Rasha.

Jirgin ya fadi ne a lokacin da ya zo sauka a sansanin soji da ke kusa da birnin Latakia da ke kusa da gabar teku a Syria.

Rasha ta ce ba harbin jirgin aka yi ba, amma binciken farko ya nuna cewa an samu matsalar na'ura ce da ta yi sanadin hatsarin.

A yanzu haka dai ana ci gaba da bincike.

A ranar 7 ga watan Janairu ne dakarun Rasha suka ce sun dakushe wani harin da aka kai da jirgi mara matuki sansanin Hmeimim.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da jiragen yakin soji na Rasha suka lalace a sansanin soji bayan da aka kai harin makamai masu linzami.

Images said to show the wreckage of the Sukhoi-25

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rasha ta ce ba harbin jirgin aka yi ba, amma binciken farko ya nuna cewa an samu matsalar na'ura ce da ta yi sanadin hatsarin