Rasha za ta kori ma'aikatan jakadancin Burtaniya 23

Laurie Bristow

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gwamnatin Rasha ta sammaci jakadan Burtaniya a kasar Laurie Bristow

Hukumomin Rasha sun ce za su kori ma'aikatan jakadancin Burtaniya 23 daga kasar a lokaci da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu sakamakon harin guba da aka kai kan tsohon ma'aikacin leken asirin Rasha da 'yarsa a London.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce za ta kori 'yan kasar ta Burtaniya a mako daya.

Ta kara da cewa za ta rufe cibiyar raya al'adun Burtaniya, British Council, da ke Rasha sannan ta yi watsi da damar da ta bai wa Burtaiya ta bude karamin ofishin jakadancinta a St Petersburg.

Mahukuntan Rasha sun dauki matakin ne bayan gwamnatin Burtaniya ta kori ma'aikatan jakadancin Rasha 23 daga Burtaniya.

An ce su fice daga kasar ne bayan abin da ya faru ranar hudu ga watan Maris, wanda Burtaniya ta dora alhakinsa kan Rasha.

A wata sanarwa da ma'aikatar wajen Rasha ta fitar ta yanke shawarar rufe cibiyar raya al'adun Burtaniya a Rasha kana ta yi watsi da damar da ta bai wa Burtaiya ta bude karamin ofishin jakadancinta a St Petersburg.

Har yanzu tsohon jami'in leken asirin Rasha Sergei Skripal, mai shekara 66, ada 'yarsa Yulia Skripal, mai shekara 33, na kwance magashiyan a asibiti, bayan an gano su cikin mummunan hali a kan wani benci a Salisbury da ke Wiltshire.

Gwamnatin Burtaniya ta ce an watsa musu wata guba da ke kashe laka da aka kirkira a Rasha mai suna Novichok, sanna Firai Minista Theresa May ta ce ta yi amanna mahukuntan Rasha na da hannu a lamarin.