Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka: Ana asarar rayuka masu yawa ga makamai
Dubban Amurkawa sun fita kan tituna a wasu biranen kasar don neman a rika daukar tsauraran matakai akan mallakar bindigogi.
Taken masu zanga-zangar shi ne "muna machi ne don rayuwar mu".
Jagororin su sune wasu daga cikin mutanen da suka tsira a harin bindiga da aka kai watan da ya gabata a wata makaranta da ke Florida inda aka hallaka mutane 17.
Zanga-zanga mafi girma shi ne wanda aka gudanar a birnin Washington - baya ga wasu jihohin a fadin kasar.
Wasu shahararru mawaka kenan wadanda suka hadu da dalibai da malamai rike da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce da ke cewa "a kare daliban mu ba bindigogi ba".