Buhari na shan yabo da suka kan 'yan matan Dapchii

Boko Haram Dapchi

Asalin hoton, Sahara Reporters

Lokacin karatu: Minti 4

Muhawara ta barke a shafukan sada zumunta na Najeriya sa'o'i kadan bayan da mayakan kungiyar Boko Haram suka sako mafi yawan 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi 110 da suka sace ranar 19 ga watan Fabrairu.

A yayin da wasu da dama ke yabon gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jajircewa wajen cika alkawarin da ta dauka na ganin ta ceto yaran, wasu kuwa nuna shakku suke a kan wannan lamari.

Da dama sun yi ta wallafa ra'ayinsu a shafukan Twitter da Facebook, inda suke cewa tun farko sace yaran ma 'kitsa' shi gwamnatin ta yi don neman farin jini wajen jama'a.

Wasu kuwa sun yi ta yaba wa kokarin gwamnatin ne amma a hannu guda kuma suna kira gare ta da ta dauki matakan magance faruwar irin haka a gaba.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

JJ Omojuwa wani fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta ne a Najeriya, ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter cewa: Ya kamata a ce an dauki lokaci kafin a dawo da yaran idan aka yi la'akari da matakan hanyoyin da za a yi hakan. Abu ne mai kyau a san me gwamnati ta bayar ko ta yi a wannan karon kafin a sako yaran nan.

''Mun ji dadin dawowarsu amma ka da mu manta da daukar mataki don gudun sake afkuwar hakan a gaba.''

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wasu kuwa da dama tababa suke kan yadda Boko Haram suka shiga garin Dapchi ido na ganin ido suka mayar da yaran nan, ba tare da jami'an tsaro sun tare su ba.

Kemi Ariyo @d_problemsolver ya rubuta cewar: "Boko Haram suka taho tun daga dajin Sambisa har garin Dapchi don mayar da yaran nan kuma a ce ba wanda ya gansu?

"Lallai ga alama batun Boko Haram da na rikicin Fulani da Makiyaya duk farfagandar siyasa ce. Abun takaici!"

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Sai dai wani ma'abocin amfani da shafin Facebook Sheriff Almuhajir ya yi wani batu mai kamar martani ga maganar Mista Ariyo inda yake cewa: "Wai wasu sun dauka tunda Boko Haram sun kawo 'yan mata kawai sai a kama harbe su.

"Hmmmm! Kun dauka su Boko Haram mahaukata ne za su kawo su haka kawai babu sharadi, shiri ko togaciya? Ina jin wasu mutanen ta hanci suke tunani."

Wannan layi ne

Dr Aliyu Tilde kuwa yabo da jinjinawa ya yi wa Shugaba Buhari kan ceto 'yan matan.

Ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa: "Wannan lamari ne mai dadi ga iyayen yaran sannan abun a jinjinawa Shugaba Buhari ne, wanda ya yi barazanar gurfanar da kwamandojin sojin a gaban kotun sojoji."

A ganin Dr Tilde ko da fansa aka biya aka karbo yaran, to hakan ya fi don su dawo gida da wuri maimakon a tsaya jiran shekaru.

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, JIM WATSON

Ya kara da cewa a ganinsa ko da fansar aka biya, iyayen yaran za su zabi haka fiye da zama cikin zulumi.

A karshe ya bai wa gwamnati shawarar cewa ya kamata ta kara tsaurara tsaro a yankin arewa maso gabas ta yadda mayakan Boko Haram ba za su iya amfani da injin fidda kudi na ATM ba.

Wannan layi ne

Wannan batu dai zai ji gaba da jan hankalin 'yan Najeriya a ciki da wajen kasar har zuwa wani lokaci.

Sai dai a yayin da aka samu damar ceto 'yan matan na Dapchi, har yanzu akwai sauran 'yan matan sakandaren Chibok da aka sace tun 2014 a hannun mayakan Boko Haram, duk da cewa fiye da rabinsu sun dawo.

Wannan layi ne

Sharhi: Daga Tomi Oladipo, wakilin BBC kan sha'anin tsaro a Afirka

map

Dawowar 'yan matan Dapchi da aka sace ya nuna cewa Boko Haram ta sauya salo karkashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi.

Kungiyar masu tayar da kayar bayan dai ta kasu biyu, daya karkashin shugabancin Abubakar Shekau daya kuma karkashin al-Barnawi, wanda kungiyar IS ke marawa baya.

A baya, Shekau ya ki yarda ya sasanta da gwamnatin Najeriya, musamman kan batun sako 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace a shekarar 2014.

A bayyane yake cewa a wannan karon bangaren al-Barnawi sun shirya sasantawa da gwamnati, kuma 'suna da yakinin' samun wani abu daga gwamnatin a matsayin fansa.

Matsalar ita ce ba abun da zai hana mayakan sake kai hari wata makaranta ko al'umma nan gaba, tare da sace wasu mutanen da nufin sake cika lalitarsu.

Wannan bahaguwar dabara ce ka karawa kungiyar da ka ke kokarin murkushewa karfi ta hanyar biyansu fansar kudi ko mayar musu da kwamandojinsu da ke hannun hukuma.

Amma gwamnatin Najeriya ta gwammace ta guji zubewar kimarta a idon duniya, kamar yadda ya faru da gwamnatin tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan, kan yadda ya ki daukar batun sace 'yan matan Chibok da muhimmanci.

Karanta karin labarai masu alaka

Amma shi ma abun da ya faru na sace 'yan matan Dapchi yana cike da "sakaci".

Da farko hukumomi sun yi watsi da batun sace 'yan matan, (har ma suka yi wa iyayen yaran da suka yi ikirarin hakan barazana) sai kuma daga baya suka ce an ceto yaran.

Wannan ya jawo bacin rayuka a al'ummar da abun ya shafa. Shugaba Buhari ya yi kokarin ziyartar yankin da kuma yin alkawarin cewa gwamnati za ta yi duk abun da ya dace don ceto yaran.

Ceto yaran Dapchi dai zai kwantar da hankalin 'yan matan da iyayensu da masoyansu, amma kuma zai ja wa gwamnati farin jini ne dan kadan.

Ga alama dai wadannan masu tayar da kayar bayan ba su da wata asara a wannan lamarin, kuma Boko Haram za ta ci gaba da zamowa annoba ga Najeriya da makwabtanta na yankin Tafkin Chadi.