Taron addu'o'in jagoran 'yan adawa a Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya mika ta'aziyyarsa bisa ga rashin da aka yi na jagoran 'yan adawa, Morgan Changirai, wanda ya mutu sakamakon cutar kansa a makon da ya gabata.

Mr Mnangagwa, ya bayyana marigayin a matsayin wani muhimmi a siyasar kasar wanda kuma ya dace a rinka tunawa dashi a tarihin kasar.

Daga nan ya yi kira ga al'ummar kasar da su hadu domin nuna alhininsu ga babban rashin da aka yi.

Taron aduu'oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.

Kazalika daruruwan magoya bayan 'yan adawar kasar sun taru a wajen cocin, sanye da jajayen kaya, launin jam'iyyarsu.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Allah ya yi wa Tsvangirai rasuwa yana da shekara 65 a duniya.

A ranar Talata ne za a binne gawarsa a kauyensa da ke Buhera.