Kun san shugabannin "bogi" na kasashen Afirka?

Asalin hoton, EPA
A ranar Talata ne jagoran 'yan hammayya na kasar Kenya Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, bayan da ya sha kaye a zaben da aka sake gudanarwa a watan Oktobar shekarar da ta gabata.
Ba wannan ne dai karo na farko da wani ya taba rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa ba a nahiyar Afrika bayan shan kaye a zabe.
A wannan makala dai mun kawo muku jerin mutanen da suka taba kokarin rantsar da kansu a matsayin shugabannin kasa a nahiyar.
A Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo akwai Etienne Tshisekedi da Moshod Abiola a Najeriya, da Kiza Besigye na Uganda, da kuma Jean Ping na Gabon.
Wadannan nan daga cikin jagororin hamayya na kasashen Afirka wadanda suka yi kokarin ayyana kansu a matsayin shugabannin kasashensu, bayan kuma a lokacin kasashen suna da shugabanni da ke kan kujera. A ranar talatar nan Raila Odinga, shugaban 'yan hamayya na Kenya ma ya bi layin wadannan 'yan siyasa.
A Uganda jagoran 'yan hamayya na kasar Dakta Kizza Besigye, wanda ya dade yana adawa da Shugaba Yoweri Museveni, ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar, inda aka nuna bidiyon rantsuwar da aka yi a wani wuri na sirri a shekarar 2016, kwana daya kafin rantsar da Museveni.
Daga baya an kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, inda aka rika gurfanar da shi a gaban shari'a.
Etienne Tshisekedi shi ne shugaban 'yan hamayya a lokacin mulkin Shugaba Mobutu Sese Seko na Zaire, kasar da shi kuma Laurent Kabila ya sauya wa suna zuwa DRC (Jamhuriyra Dumokuradiyyar Congo), daga baya kuma har zuwa yanzu ta kasance karkashin dansa Joseph Kabila.
Wata kamanceceniya tsakanin Tshisekedi da Odinga ita ce, dukkaninsu an taba tsare su ba tare da an yi musu shari'a ba, sannan kowanne cikinsu ya taba zama Firaiminista, kuma duka sun kaurace wa zaben shugaban kasa; Tshisekedi a 2006 sannan Raila a 2017.
A watan Nuwamba na 2011, Tshisekedi ya yi takara ya kalubalanci dan Laurent Kabila kuma ya zama na biyu a zaben. Daga nan sai ya shirya karbar rantsuwa a matsayin shugaban kasa, a wani biki da ya shirya a garinsu, karkashin shugaban ma'aikatansa Albert Moleka bayan da kokarin ganin an rantsar da shi a filin wasa na Martyr a babban birnin kasar, Kinshasa ya ci tura.
Daga bisani an yi masa daurin talala a gidansa.
A Najeriya, Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa lokacin Sani Abacha na kan mulki. Ya yi hakan ne bayan da ya ziyarci kasashen Turawa na yammacin duniya, yana neman goyon bayansu a kan gwamnatin Abacha. An kama shi aka tuhume shi da laifin cin amanar kasa, sannan aka yi masa daurin shekara hudu, zuwa shekara ta 1995.
A 2016 a Gabon, shugaban 'yan adawa Jean Ping ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, kuma ya bukaci da a sake kirga kuri'un zaben shugaban kasar, kirgen da aka sake yi ya tabbatar da Shugaba Ali Bongo mai ci a matsayin wanda ya yi nasara. sai dai duk da haka, Ping ya kafe yana cewa, ''ai duk duniya ta san shi ne shugaban kasar."










