An yi mummunar gobara a Kenya

Asalin hoton, Reuters
An bayar da rahoton cewa dubban mutane ne suka rasa gidajensu bayan da wata gobara ta mamaye gidajen unguwar marasa galihu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum hudu.
Mazaunan yankin sun yi amfani da ruwan amfaninsu na yau da kullum a kokarin da suke na kashe gobara, wacca ta mamaye gidajensu da ke yankin Lang'ata a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Dan majalisar da ke wakiltar yankin, Nixon Korir ya ce, babu wadataccen ruwa ne a injin da ake amfani da shi wajen kashe gobarar.
Wutar ba ta daina ci ba sai da misalin karfe 06:00 na safiyar Litinin agogon kasar.
'Yan sanda sun fara gudanar da bincike game da gobarar wacce ta fara ci da misalin karfe 8:00 na ranar Lahadi, inda ta shafe sa'a goma tana ci.

Asalin hoton, Reuters
Ba wannan ne karon farko da aka rasa ruwa a injin kashe gobarar ba.
Kuma idan za a zuba a ruwa a cikin injin sai an yi tafiya mai nisan kilomita 20 daga yankin Kijiji kafin a dawo cikin garin.
Pius Masai shi ne shugaban hukumar kula da annoba ta kasa, ya ce, yankin ba su abin kashe gobara.
Mazaunan yankin sun shiga tashin hankali, inda suke amfani da duk wani da hannunsu zai kai wajen kashe gobarar.
Wanda ya hada da ruwan da suke amfani da shi a gida na yau na kullum.
Injinan kashe gobara hudu kawai a kai musu. Wanna kuwa ya yi kadan a yankin da aka bayar da rahoton kusan mutum 6,000 suka rasa muhallansu.
An samu tambayoyi da dama da suke cewa me ya sa hukumomi ba su tura wadansu karin injinun ba.
Sojin kasar Kenya sun saba kai wa farar hula dauki a lokacin da wata annoba ta taso.
Amma a wannan lokacin sojoji ba su kai dauki, kodayake barikin sojin Langata na da tazara kadan daga yankin.
Sai dai ba a san dalilin rashin zuwansu wannan lokacin ba, alahali za su iya hango tashin gobarar daga inda suke.











