Bangladesh 'za ta mayar da Musulmin Rohingya 300' Myanmar

Hukumomi a Bangladesh sun ce sun amince kan wata yarjejeniya da takwarorinsu na Myanmar domin mayar da dubban daruruwan Musulmi 'yan kabilar Rohingya wadanda suka tsere daga Myanmar din sakamakon kisan da sojojin kasar suka yi musu a shekarar da ta gabata.

Myanmar ta amince ta karbi 'yan Rohingya 1,500 akowanne mako, in ji Bangladesh, tana mai cewa tana sa ran mayar da dukkaninsu Myanmar nan da shekara biyu.

Fiye da 'yan Rohingya 650,000 suka tsere zuwa Bangladesh tun lokacin da aka soma kashe su a jihar Rakhine a watan Agustan da ya wuce.

Kungiyoyin bayar da agaji sun bayyana damuwa kan yunkurin komawa da su ta karfin tsiya.

Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya ce akwai bukatar Myanmar ta magance abin da ya haddasa rikicin, yana mai cewa 'yan gudun hijirar za su koma gida ne kawai idan suka gamsu da samun tsaron.

Kamafanin dillancin labarai na Reuters ya ce yarjejeniyar ba ta fayyace lokacin da za a soma mayar da mutanen gida ba, amma ta ce Myanmar za ta bayar da matsugunin wucin-gadi ga mutanen kafin ta gina musu gidaje.