An kama mutumin da ya yi jima'i da akuya a Kenya

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Kenya sun tuhumi wani mutum bisa zargin yin jima'i da wasu akuyoyi biyu na makwabcinsa.
An zargi mutumin, mai shekara 35, da laifin kisan akuyoyin bayan ya gama jima'in da su.
Masu shigar da kara sun gabatar da mushen akuyoyin a gaban kotun Kangundo da ke gabashin birnin Nairobi a matsayin shaida,abin da ya girgiza mutanen da ke cikin kotun.
Mutumin ya shaida wa kotun cewa 'yan sandan da suka kama shi sun lakada masa duka sannan suka azabtar da shi.
Alkalin kotun ya ba da umarni a kai mutumin asibit domin a binciki lafiyarsa saboda zargin dukan da ya ce an yi masa sannan ya ba da belinsa a kan $1,000ko kuma ya samu mai tsaya masa a madadin hakan.
Za a ci gaba da sauraren karar ranar 29 ga watan Janairun 2018.
Dokokin kasar Kenya sun bukaci a daure mutum tsawon shekarar 14 idan ya aikata irin wannan laifi.
Ba wannan ne karon farko da aka samu mai aikata irin wannan laifi ba.
A watan Maris din da ya gabata, an daure wani mutum tsawon shekara 15 bayan an same shi da laifin yin jima'i da kaza a yammacin kasar, inda ya ce yana matukar tsoron yin mu'amala da mata.










