Bostwana ta rufe Cocin da fasto ke 'yawo kan iska'

Lokacin karatu: Minti 2

Botswana ta rufe cocin wani fasto dan asalin kasar Malawi, wanda ya haifar da rudani a kasar bayan ikirarin cewa yana yawo kan iska.

Faston mai suna Shepaerd Bushiri, gwamnati ta tabbatar da rufe cocinsa da ake kira Enlightened Christian Gathering Church (ECG) a Gaborone, saboda fargaba kan abin da gwamnatin ta kira wurin samun kudin tsafi.

Rahotanni sun ce cocin ta shigar da kara domin kalubalantar matakin, wanda ke zuwa kasa da shekara guda bayan an haramta wa faston shiga kasar.

Sai dai ministan Bostwana Edwin Batshu a watan Afrilun 2017 ya taba sanar da cewa Mista Bushiri da yanzu ke zaune a kasar Afirka ta kudu, sai ya nemi biza kafin shiga kasar, duk da cewa 'yan Malawi ba su bukatar biza, kamar yadda kafar AllAfrica.com ta ruwaito.

Presentational grey line

Shin wanene Shepherd Bushiri?

  • Dan asalin Malawi ne, kuma ya mallaki coci-coci a Ghana da Afrika ta kudu
  • Ya yi ikirarin yana warkar da masu dauke da cutar HIV, kuma yana rayar da matacce, kamar yadda jaridar Mail & Guardian ta ruwuito.
  • Ya taba hasashen cewa Birtaniya za ta rabu kuma za ta fada cikin rikici, kamar yadda jaridar Maravi Post ta ruwaito
  • Ya fito a wani faifan bidiyo wanda ya ja hankali a kafofin sadarwa inda ya yi ikirarin yana tafiya saman iska
  • Ya shaida wa Kembo Mahdi dan siyasa a Zimbabwe cewa zai sami mukami kafin a nada shi mataimakin shugaban kasa, a cewar jaridar New Zimbabwe
Presentational grey line

Jaridar ta kuma kara da cewa cocin na amfani da kudaden tsafi, wanda hakan kuma ya sabawa dokokin kasa.

Mista Bushiri yana da mabiya sama da miliyan 2.3 a shafin Facebook, kuma mutane sun taba cika makil a wani taronsa da aka gudanar a filin kwallon kafa na FNB a Johannesburg jajibirin kirsimeti.

Faston ya taba fuskantar suka a lokacin da ya bukaci a biya kudi tsakanin dala 80 zuwa dala 200 domin shiga kallon wani kasaitaccen bikinsa a Afrika ta kudu.