Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe dalibi a zanga zangar karin farashin biredi
An kashe wani dalibi cikin masu zanga-zanga a kan karin farashin biredi a yankin Darfur na kasar Sudan.
Tun bayan da gwamnati ta sanar da janye tallafi a kan kudin fulawa da ake amfani da shi wajen yin biredi ake ta zanga-zanga a wasu yankuna na kasar ciki har da Khartoum, babban birnin kasar.
'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa gungun masu zanga-zanga wadanda suke ta jifa da duwatsu tare da kona tayoyi.
Haka kuma masu zanga-zanga sun rufe wasu hanyoyi a yammacin Darfur.
Wani karamin ministan ya yi gargadin cewa za'a hukunta duk masu zanga zanga da suka lalata kayayyaki.
Hukumomi sun kwace kofi-kofi na wasu jaridun kasar wadanda suka soki karin farashin biredin.
Gwamnatin Sudan ta ce fiye da mutum 80 ne suka mutu a shekarar 2013 sakamakon zanga zanga da aka kwashe makonni ana yi a kasar saboda janye tallafin man fetur.