Za a haramta wa mata masu bilicin aikin yi a Ghana

Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bilicin na lalata fata

Hukumar shige da fice a Ghana ta ce ta soke cancantar matan da fatar jikinsu ta nuna suna bilicin daga cikin sabbin ma'aikatan da za ta dauka aiki.

Hukumar ta ce daukar matakin ya zama wajibi saboda dalilai na tabbatar da lafiyar jami'anta.

Kakakin hukumar Michael Amoako-Attah ya shaida wa BBC cewa an dauki matakin ne domin kare lafiya da jin dadin jami'an hukumar.

Hukumar ta ce matan da ke bilicin na iya fuskantar matsalar zubar jini a jikinsu, wanda kuma kalubale ne ga lafiyarsu.

A baya dai an sha cin karo da matsalar a yayin atisayen daukar sabbin ma'aikata.

Mista Amoako-Attah ya ce yanzu suna kokarin ganin sun kaucewa sake fuskantar matsalolin.

Mata idan sun fara shafe shafe, fatarsu takan yi haske da laushi amma daga baya za su fuskanci matsaloli inda fatar jikinsu ke canza kamanni.

Ghana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Fatar mata na canza kamanni saboda bilicin

Sai dai matakin da hukumar ta Ghana ta dauka bai shafi Maza masu gashin dada ba, irin yanayin gashin Bob Marley.

Dubban mutane ne suka nemi aikin da hukumar za ta dauki jimillar ma'aikata 500 inda hukumar shige da ficen ta Ghana ta ce ta tantance sunayen mutane 84,637.

Kuma duk mutum guda sai da ya biya kudin Ghana Cedi 50, kwatankwacin $11, inda a jimilce hukumar za ta samu makudan kudi da suka kai $880,000.

Wasu 'yan Ghana dai sun yi kira ga shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya shiga tsakani.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokoki sun bukaci matan da matsalar ta shafa su kai kokensu a Kotu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mata ke fuskantar wariya saboda yanayinsu ba a Ghana.

Wasu hukumomin tsaro sun sha kin daukar aiki matan da suke ganin suna da girman mama.