Kalli hotunan yadda 'yan Shi'a suka yi tattaki a Ghana

Kamar sauran takwarorinsu a duniya, mabiya Shi'a a Ghana sun yi tattakin Arbaeen wato tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Hussain, ya shiga a karni na bakwai.

Mabiya Shi'an sun yi tattakin ne a karkashin jagorancin kungiyar Shi'a Youth of Ghana
Bayanan hoto, Mabiya Shi'an sun yi tattakin ne a karkashin jagorancin kungiyarsu mai suna, Shi'a Youth of Ghana
Ana tattakin ne don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW) Imam Hussain ya shiga a karni na bakwai
Bayanan hoto, 'Yan Shi'a suna tattakin ne don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW) Imam Hussain ya shiga a karni na bakwai
Daruruwan 'yan kungiyar ne suka rika kewaye wadansu titunan birnin Accra ranar Asabar da safe
Bayanan hoto, Daruruwan 'yan kungiyar ne suka rika kewaye wadansu titunan birnin Accra ranar Asabar da safe
Sun faro tattakin ne daga wani masallacinsu da ke unguwar Mamobi a Kwanka Bus Stop zuwa filin Ojo a birnin Accra
Bayanan hoto, Sun faro tattakin ne daga wani masallacinsu da ke unguwar Mamobi a Kwanka Bus Stop zuwa filin Ojo a birnin Accra
Cikin wadanda suka fito tattakin har da jagororin kungiyar
Bayanan hoto, Cikin wadanda suka fito tattakin har da jagororin kungiyar
Wadansu mambobin kungiyar
Bayanan hoto, Mambobin kungiyar sun rika rera wakokin nuna alhininsu ga Imam Hussain da kuma kiran sunansa
Wani jami'in tsaro
Bayanan hoto, Jami'an tsaro sun yi musu rakiya don tabbatar da tsaro yayin tattakin
Mabiya Shi'an sun yi tattakin ne a karkashin jagorancin kungiyar Shi'a Youth of Gahana
Bayanan hoto, Galibin masu tattakin matasa ne da mata da kuma kananan yara
Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin Jagoran mabiya Shi’a a Ghana,
Bayanan hoto, Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin jagoran mabiya Shi’a a Ghana, yana barin wurin bayan kammala tattakin