Nigeria: An jefi gwamnan jihar Benue kan makiyaya

Asalin hoton, Benue State Government
Masu zanga-zangar kin jinin hare-haren da ake kaiwa a jihar Benue sun jefi gwamnan jihar a lokacin da ya nemi yi musu jawabi .
Shaidu dai sun ce masu zanga-zangar sun bazu cikin garin Makuridi ne domin nuna rashin jin dadinsu game da hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Benue da ke tsakiyar Najeriya.
Masu zanga-zangar suna kira ne ga shugaban Najeriya ya dakile hare-haren da ake kai wa jihar Benue din ko kuma ya yi murabus.
Gwamnatin jihar Benue dai ta ce an kashe akalla mutum 33 a hare-haren da aka kai kauyukan jihar da ke garin Guma.
Gwamnan jihar, Samuel Ortom, dai daga garin na Guma ya fito.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Lawrence Onoja, ya shaida wa BBC cewa an fara kai hare-haren ne ranar farko ta sabuwar shekara kuma aka ci gaba da kaiwa har zuwa safiyar Talata.
Baya ga mutum 20 da kwamishinan ya tabbatar an kashe a hare-haren da ya ce makiyaya ne suka kai, an kona gidaje da dama kuma mutane da yawa sun tsere daga gidajensu.
Kawo yanzu dai kungiyar makiyaya ta Najeriya ba ta ce komai ba game da harin da aka daura wa makiyaya alhakin kaiwa.
A kwanakin baya ne dai gwmamnatin jihar Benue ta kaddamar da dokar hana kiwo a fili.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu makiyayan sun yi na'am da dokar hana kiwo ta jihar Benue din yayin da wasu suka ki amincewa da ita.











