Dino Melaye ya fito a wakar hip-hop

Asalin hoton, Youtube/Uche Kachikwu
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Dino Melaye, ya fito a bidiyon wata wakar hip-hop da dan karamin ministan man fetur na Najeriya.
A bidiyon mai tsawon minti uku da dakika 48 an nuna motoci na alfarma da lambar mota ta musamman mai dauke suna Dino.
An kuma yi ta watsa dalar Amurka dari-dari yayin da matan da suka yi shigar da ke nuna tsiraici suke rawa da maza.
Bidiyon dai da ya nuna kwarangwal na zinari da kuma mutane suna yi kamar suna cin dalar Amurka, kuma Dino ya fito daga wata mota sanye da riga da ke dauke da rubutu "Legend", wato gwarzo a harshen Ingilishi.
A makon jiya ne dai Sanata Dino Melaye ya wallafa kadan daga cikin bidiyon.
Tuni dai bidiyon ya fara jan hankalin 'yan Najeriyar, yayin da wasu suke yin Allah-wadai da bidiyon, wasu cewa suke wannan ba wata matsala ba ce.

Asalin hoton, Youtube/Uche Kachikwu

Asalin hoton, Twitter/@ogundamisi
Sai dai kuma mawakin da ya yi wakar, Uche, dan ministan man Najeriya, Ibe Kachikwu, ya ce sanatan ya fito ne a bidiyon domin ya ba shi karfin gwiwa.
Ya ce: "Ba wai ya fito da mata ko kuma ba wai ya wakilci Najeriya ba ne a bidiyon."

Asalin hoton, Youtube/Uche Kachikwu
Mawakin dai ya musanta cewa mukamin babansa ne ya sa Sanata Melaye ya fito a bidiyon, yana mai cewa shi ya tsani a hada cigabansa a fagen waka da mukamin babansa.










