An sauke kwamandan rundunar yaki da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta sauke kwamandan da ke jagorantar yaki da kungiyar Boko Haram a kasar daga kan mukaminsa.

Hakan ya biyo bayan yawan hare-haren da 'yan kungiyar ke kai wa ne a baya-bayan nan, wadanda suka hada da wani hari da aka kai masallaci a garin Mubi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 50.

Ba a dai bayar da wani dalili a hukumance na sauke Manjo Janar Attahiru Ibrahim ba.

Babban hafsan rundunar sojin kasa Tukur Buratai, ya ba shi wa'adi a watan Yuli don ya kawo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a raye ko a mace cikin kwana 40.

A kalla mutum 20,000 aka kashe, yayin da kungiyar ta sace wasu dubbai, tun lokacin da kungiyar ta fara ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama mulki ne a watan Mayun 2015, inda ya yi alkawarin murkushe mayakan.

Bayan wata bakwai da hawansa ne, ya ayyana cewa an yi nasara a yaki da kungiyar, bayan da sojoji suka kwato mafi yawan yankunan da ke karkashin ikon mayakan.

Sai dai kuma Boko Haram ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a arewa maso gabshin kasar.

A watan Yuli ma, fiye da mutum 40 ne suka mutu a yayin wani aiki da sojoji suka yi don tserar da mutanen da mayakan Boko Haram suka yi wa kwanton-bauna a wani ayarin motoci.

Wadanda suka mutun sun hada da sojoji da wata tawagar masu hakao mai.

An nada Manjo Janar Attahiru Ibrahim ne don ya jagoranci yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya a watan Mayun wannan shekarar.

Ya maye gurbin Janar Nicholas Rogers ne, wanda ya jagoranci wata rundunar hadin gwiwa ta musamman ta sojoji da 'yan sanda, don dakile rikicin kabilanci a yankin tsakiyar Najeriya.

Boko Haram a takaice

  • An kafa ta a shekarar 2002
  • Sunanta da Larabci shi ne, Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad
  • Ta fara aikinta ne da nuna kin jinin karatun boko
  • Ta kaddamar da kai hare-hare a shekarar 2009 da zummar samar da daular musulunci
  • Amurka ta ayyana ta a matsayin kungiyar ta'adda a 2013
  • Kungiyar ta ayyana wasu yankuna da ta kame a matsayin daulolin musulunci a shekarar 2014
  • A yanzu haka sojoji sun kwato mafi yawan yankunan