Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe gomman mutane a Mubi
A kalla mutum 50 ne suka mutu bayan da wani ya kai harin kunar bakin wake a wani masallaci da ke cikin garin Mubi a jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya.
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ce ta tabbatar wa BBC Hausa yawan mutanen da suka mutu a harin.
Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina a cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar asubahin ranar Talata.
Dan kunar bakin waken yana tsakiyar jama'a ne lokacin da ya tayar da bam dinsa bayan an tayar da Sallah.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga Sashen Hausa na BBC, kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajo, ya ce hukumomi ba za su iya tabbatar da iya adadin wadanda suka mutu a harin ba tukunna.
Ya kara da cewa da yawa daga cikin mutanen da abin ya rutsa da su gabobin jikinsu sun tarwatse, saboda haka zai yi wuya a gane adadinsu.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta tura ma'aikatan kiwon lafiya garin na Mubi domin yi wa wadanda lamarin ya shafa magani na gaggawa da kuma ceton rayuka.
Wannan ne karon farko da aka kai hari da ya kai haka muni garin na Mubi, tun bayan sojojijn Najeriya sun kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram.
Mayakan Boko Haram dai sun kwace garin Mubi ne a shekarar 2014, amma daga baya sojojin Najeriya suka kwato garin daga hannunsu.
Hare-haren kunar bakin wake dai na faruwa a baya-bayan nan musamman ma a jihar Borno, al'amarin da ke kara tayar da hankalin jama'a.