An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a kusa da ofishin hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka ce.

Sai dai a cewar shugaban hukumar Injiniya Satomi Ahmad, 'yar kunar bakin waken ce kawai ta rasa ranta a lamarin wanda ya faru da yammacin Asabar.

Mutum 14 ne suka mutu a makon jiya baya ga 'yan kunar-bakin-wake uku sanadiyyar wani harin da aka kai Muna Garage a wajen birnin Maiduguri.

Karanta wadansu karin labarai