An kai harin kunar bakin wake Maiduguri

Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mako guda ke nan da kai wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 14

Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a kusa da ofishin hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka ce.

Sai dai a cewar shugaban hukumar Injiniya Satomi Ahmad, 'yar kunar bakin waken ce kawai ta rasa ranta a lamarin wanda ya faru da yammacin Asabar.

Mutum 14 ne suka mutu a makon jiya baya ga 'yan kunar-bakin-wake uku sanadiyyar wani harin da aka kai Muna Garage a wajen birnin Maiduguri.

Karanta wadansu karin labarai