'Yan fashi sun sa mutane tsere wa kauyukansu a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Mazauna kauyukan Batoli da Kuka 9 da Tafkin Dawaki da kuma Gidan Sarauta a cikin jihar Zamfara sun tsere zuwa daji sakamakon wani wa'adi da wasu da ake zargin 'yan fashin shanu ne suka ba su don su fanshi kansu.
An dai ba wa mazauna kauyukan zuwa ranar Juma'a don su biya naira miliyan biyu ko kuma su fuskanci farmaki.
Haka zalika an shaida wa BBC cewa su ma mutanen kauyukan Gidan Rana da Babu Dole da Gidan Saleh a cikin karamar hukumar Isan jihar Sokoto, sun shiga irin wannan tsaka mai wuya bayan an ba su wa'adin zuwa ranar Litinin da ta gabata.
Wasu mutanen kauyukan da suka tsere sun fada wa wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza ta wayar tarho daga mafakarsu cewa suna cikin mawuyacin hali don kuwa ko abin da za su ci ma wahala yake yi musu ballantana su iya tara naira miliyan biyu a matsayinsu na talakawa.
Daya daga cikin mutanen wanda ba a ambaci sunansa ba ya ce: "Sunka ce ko mu ba su miliyan biyu zuwa Juma'a, ko su zaka su kakkashe mu, su kone muna gari."
"To shi ne ga yanzu muna bakin daji, duka garin mun watce, ba kowa. Abincin ma da za mu ci babu, ba kowa garin namu."
Shi ma abokin gudun tsiransa ya ce: "Abubawan da ke damunmu dai a halin yanzu shi ne, matsala ta barayin shanun nan."
"Sabadda ka ga sun nuna sai mun ba su kudi, naira kusan miliyan biyu, to mu kuma alhali abincin da za mu ci ma, ya mana wahala. To shi ne gabaki daya suka ba mu notis zuwa Juma'a."
Mutanen ba su dai fayyace ko sun fito ne daga kauye daya ne ko kuma kauyukansu daban-daban ne ba.
Rikicin barayin shanu dai ya addabi yankunan jihar Zamfara, inda ko a ranar 19 ga wannan wata na Nuwamba wasu da ake zargin barayin shanu ne sun kashe fiye da mutum 50 a hare-hare mabambanta da aka kai kauyukan Faro da Kubi da Shinkafi a jihar.
Mazauna yankunan sun ce, ana zaman dar-dar saboda maharan sun auka wa kauyukansu inda suka far wa mutane, abin da ya sa wasu da dama suka gudu don tsira da rayukansu.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara dai ta ce ba ta da masaniya game da halin da mazauna kauyukan suke ciki.
Sai dai, mahukunta a nasu bangare cikin jihar Sokoto sun ce tuni sun dauki matakan tura jami'an tsaro zuwa yankunan da ke fama da wannan al'amari.
Shugaban karamar hukumar Isa, Kanal Garba Moyi (Murabus) ya ce sun fada wa jami'an tsaro kuma sun kara musu man fetur a motoci, inda ya ba da tabbacin cewa yanzu haka suna kauyukan da aka tura su.











