Nigeria: An kashe mutum fiye da 50 a Zamfara

Asalin hoton, NIGERIA ARMY
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Nigeria, na cewa an fara komawa zaman zullumi sakamakon dawowar hare-haren masu satar shanu da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Mazauna garin Faro da Kubi da Shinkafi a jihar sun ce, ana zaman dar-dar saboda wasu mahara sun shiga garin inda suka far wa mutane.
Fiye da mutum 50 ne mazauna garuruwan suka ce sun mutu a hare-hare mabambanta da aka kai kauyukan, inda mutane suka gudu don tsira da rayukansu.
Sarkin Shanun Shinkafi Dakta Sulaiman Shu'aibu ya shaida wa BBC cewa, cikin daren Jumma'a ne mutanen da ake zargin suka je wani kauye mai suna Tunga Kabau, suka kashe mata 25 da kuma maza tara.
Daga nan ne kuma suka bankawa kauyen wuta.
Bayan nan kuma sun nufi wani kauyen da ake cewa Mallabawa, nan ma suka kashe mutum 19.
"Gaskiya ya kamata gwamnatin jihar Zamfara ta sake damara wajen kawo karshen hare-haren da masu satar shanu ke kai wa wasu kauyukansu," in ji Dakta Sha'aibu.
Su ma mazauna garin Faro da Kubi duk a jihar ta Zamfaran, sun ce kwana biyu sun dan samu sassaucin hare-haren 'yan ta'adda da barayin shanu, da kuma dauki dai-dai da ake musu.
Amma kuma tun daga makon da ya gabata hare-haren sun sake dawowa, kamar yadda suka ce.
Wani mazaunin garin Faro ya shaida wa BBC, cewa barayin shanun sun yi mummunar barna da ta hada da asarar rayuka da kona musu amfanin gona.
Hare-hare da aka kai wasu kauyukan jihar Zamfara, na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ke cikin tashin hankali, sakamakon dawowar hare-haren kunar bakin wake a jihar.
A baya dai hukumomi da jami'an tsaron na cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya.
Ko a ranar Asabar ma wadansu 'yan kunar bakin wake mata hudu sun kai hari a wajen birnin Maiduguri, inda suka kashe kansu da kuma wani yaro karami.
A makon nan mutum 18 sun rasa rayukansu sakamakon harin kunar bakin wake a birnin.
Haka zalika wadannan hare-haren na zuwa ne duk da ikirarin da rundunar sojin kasar ke yi na cewa suna samun nasara a yakin da suke yi da Boko Haram da barayin shanu da kuma ma masu satar mutane don neman kudin fansa.
- An gyara wannan labarin sakamakon kuskuren da muka yi da farko, inda muka ce mun tuntubi Mai Magana da Yawun Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Dosara, alhalin ba haka ba ne.











