Mnangagwa ya tsere daga Zimbabwe

Tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, da aka kora a ranar Litinin da ta wuce , ya tsere daga kasar saboda barazanar da ake yi wa rayuwarsa a cewar mukarabansa.

Shugaba Mugabe mai shekara 93 na zargin tsohon mataimakinsa da yunkurin kwace mulki daga hannunsa.

"ya kai ziyara coci-coci, domin a fayyace masa ranar da shugaba Mugabe zai mutu.

Sai dai an fada masa cewa shi ne zai fara mutuwa,"Mr Mugabe ya fadawa magoya bansa a ranar Laraba.

A yanzu ana ganin Grace Mugabe ce za ta gaji mijinta.

Ana sa ran cewa zaa rantsar da ita a matsayin mataimakiyar shugabar kasa a taron da jamiyyar Zanu-PF mai mulki za ta yi a watan gobe.

Mr Mugabe ya kira tsohon mataimakinsa a matsayin wanda ya hada baki da wasu kuma ya yi gargadin cewa yana da aniyyar korar wasu da ke cikin jamiyyar.

Duk da cewa Mr Mnangagwa be fito bainar jama'a ya ce komai ba kan zargin da ake yi masa amma a wata sanarwar da ke dauke da sa hannunsa ya ce ya dinga yi wa shugaba Mugabe biyaya.

Sanarwar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce yana naniyar komawa gida Zimbabwe kuma ya zargi shugaba Mugabe da matarsa da yin babakere a cikin harkokin jamiyyar ta Zanu-PF.