Matan Saudia za su fara shiga filayen kwallo

Matan Saudia sun samu 'yancin shiga filayen wasanni don kallon wasan kwallon kafa da sauransu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matan Saudia sun samu 'yancin shiga filayen wasanni don kallon wasan kwallon kafa da sauransu

A karon farko kasar Saudia za ta fara barin mata zuwa filayen wasa domin kallon wasannin da ake yi.

Wannan dai wani karin yunkuri ne na ba wa mata 'yanci a kasar.

Kamfannin dillancin labaran kasar ne ya sanar da cewa daga yanzu za a rinka barin iyalan mutum da suka hada da mata da yara su rinka halartar filayen wasanni da ke manyan biranen kasar uku, wato na Riyadh da Jedda da kuma Dammam.

Wannan sabon mataki dai zai fara aiki ne daga farkon shekara mai zuwa.

Hakan dai wata 'yar dama ce a masauratar da ake killace mata a gidaje, domin a kara fito da su don shiga a dama da su a cikin al'umma.

Kazalika wannan mataki, wani bangare ne na yunkurin da matashin yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman, ke da shi na kara habaka tattalin arziki kasar ta hanyar samar da damammaki da kuma harkokin nishadantarwa ga daukacin 'yan kasar.

Kasar Saudia dai ita kadai ce a duniya da ta hana mata tuka mota a baya.

Tun bayan sanarwar damar tuka mota ga matan kasar,hankula suka kwanta musamman a fannin masu wannan fafutuka ta neman bayar da izinin tuka mota ga mata, to sai dai kuma wasu na ganin wannan dama wata hanyace ta bude kofar neman wasu 'yancin na mata da sauransu.

Kungiyoyin kare 'yancin dan Adam, sun shafe shekaru suna kiraye-kirayen ba mata damar tuki da kansu a kasar.

Kuma hukumomi sun sha tsare matan da suka karya dokar haramcin tukin mota.