Mata za su fara ba da fatawa a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
A karon farko babbar majalisar bada shawara a Saudiyya ta kada kuri'ar amincewa da a bawa mata damar yin fatawar addini.
Majalisar ta amince da shawarar da aka gabatar, kwanaki kadan bayan janye dokar hana mata tuka mota a kasar.
Ana dai bukatar sarkin kasar ya yi wata doka da za ta samar da yawan matan da ake bukata da za su iya ba da fatawar addini.
A baya malaman addinin kasar sun sha ba da fatawowi da ke janye ce-ce ku-ce, da ake dauka cewa suna nunawa mata wariya.






