Mata 100: Shin mata na samun tsaro yadda ya kamata a duniya?

BBC 100 women

Asalin hoton, Getty Images

A wannan makon rahotannin kan shirin mata 100 na BBC za su mayar da hankali ne kan tsaron lafiyar mata a cikin ababen hawa kamar motoci, jiragen kasa da jiragen sama.

Hajiya Binta Shehu Bamalli, ita ce shugabar kungiyar Sure Start Initiative kuma ta yi wa BBC bayani a kan kalubalen da mata suke fuskanta.

"Zan ba da misali da kasar Indiya, inda zaka taras cewa a cikin jiragn kasa, ana ware wasu kujeru domin mata. Maza kan zauna a kan kujerun, amma da zarar wata mace ta shiga jirgin, sai kaga wani ya tashi ya bata kujerar," in ji Hajiya Binta Shehu Bamalli.

Ta kara da cewa: "Hakazalika a cikin jiragen kasa, akwai wadanda maza ba sa shiga, domin an ware su domin mata ne kawai."

Sai dai Hajiya Binta Bamalli ta ce a kasarta Najeriya, akwai sauran aiki ga mahukunta wajen daukar matakan kare matan.

"Tun daga filin jirgin sama zuwa tashar jirgin kasa har ma zuwa tashar mota, gaskiya ba mu da irin wannan tsarin a Najeriya."

Ta kuma bayyana cewa: "A misali, lokacin da aka fara a Daidaita Sahu a Kano, mata ne kadai ke shiga saboda don su aka kebe, amma yanzu zaka taras maza sun mamaye ababen hawan."