Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata 100: Kun san macen da ta yi zarra tsakanin mazan Nigeria?
Wannan makala ce da muka rubuta don amsa tambayoyinku a kan abin da ku ke son sani game da mace ta farko da ta fara rike mukamin shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, wato Justice Zainab Bulkachuwa. A sha karatu lafiya.
Idan ana batun ilimin 'ya'ya mata a arewacin Najeriya a shekaru kusan 50 da suka gabata, tarihi ya nuna cewa an fuskanci manya-manyan kalubale da suka hana a bai wa mata damar neman ilimi, sai dai wadanda Allah Ya tsaga da rabonsu.
A wancan lokacin an fi mayar da hankali ne kawai wajen ganin an aurar da 'ya'ya mata da zarar sun fara tasawa.
Kalilan ne suka samu damar kammala makarantar firamare ko sakandire, yayin da tsiraru suka je jami'a amma su ma yawanci daga dakin aurensu.
Justice Zainab Bulkachuwa na daga cikin wadanda suka yi sa'ar samun ilimi mai zurfi tun fiye da shekara 40 da suka gabata, kuma ta yi karatun shari'ar zamani ne a lokacin da ake ganin cewa irin wannan karatu 'haramun ne, kuma duk lauya dan wuta ne,' ba ma ga mata ba kawai har da mazan.
Shin wace ce Justice Zainab Bulkachuwa?
Wannan ita ce tambayar da mafi yawan masu sauraronmu suka aiko mana kamar su Ayuba Yayaha Isma'il Wudil da Abdulrashid Mohd Dan Ango da wasu da dama.
A hirar da muka yi da ita, ta shaida mana cewa asalin sunanta Zainab Abubakar Gidado El-nafaty, an haife ta a garin Bauchi a ranar 6 ga watan Maris shekarar 1950.
'Yar asalin jihar Gombe ce daga karamar hukumar Nafada.
"Tun ina yarinya ni mai sha'awar karatu ce kuma babana shi ya fara koya min karatun addini tun ina karama kafin daga bisani ya sani a makarantar firamare ta Tudun Wada Kaduna, a lokacin da na shekara bakwai.
"Na kammala a 1960, sai kuma na tafi makarantar sakandare ta Queen Elizabeth da ke Ilorin na kuma kammala a 1972."
Justice Zainab ta ce daga nan ne batun aurenta ya taso, duk da cewa mahaifinta ya so ta yoi ilimi mai zurfi amma manyansa suka ce lallai aure za a yi mata.
Sai dai ya dage wajen ganbin cewa lallai mijin da zai aure ta ya yi alkawarin mayar da ita makaranta bayan biki.
"Haka kuwa aka yi, duk da cewa babana bai ga aurena ba, amma mijin nawa ya cika alkwari na koma makaranta inda na karanta fannin shari'ar zamani a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, na kammala a 1975 sai na wuce makarantar koyon aikin shari'a a Lagos na gama a 1976."
Justice Zainab Bulkachuwa ta shaida min cewa ta haifi uku daga cikin 'ya'yanta a lokacin da take gwagwarmayar neman ilimi.
Wuraren da ta yi aiki
Wannan tambaya ce da jama'a da dama suka aiko mana a kan Justice Bulkachuwa kamar irin su Aminu Usman Katsina.
"Na yi aikin bautar kasa a ma'aikatar shari'a ta Kaduna, daga nan sai na fara'a aiki a kotun majistare ta Kaduna tun daga shekarar 1980 inda na dinga samun karin girma har zuwa shekarar 1985.
Daga nan kuma Justice Zainab ta koma jiharta ta Bauchi a wancan lokaci inda ta ci gaba da ayikinta a mataki-mataki har ta kai matsayin alkalin babbar kotu.
Daga bisani bayan da aka kirkiri jihar Gombe sai ta koma can a matsayin alkalin babbar kotun har zuwa watan Disambar 1998.
A shekarar 1998 ne Justice Bulkachuwa ta samu sauyin aiki zuwa kotun daukaka kara ta Najeriya a matsayin daya daga cikin alkalan kotun.
Kalubale
Ko wanne al'amari na rayuwa na cike da kalubale daban-daban, to haka abin yake ga Justice Bulkachuwa.
Ta shaida min cewa a iya tsawon rayuwarta ta samu kalubale musamman a yayin da take karatu ga aure da haihuwa.
"Wani lokaci haka na yi ta fama da laulaye-laulayen ciki ga karatu, in yi ta amai amma dole na zage damtse wajen karatu ba kama hannun yaro, kuma cikin ikon Allah ban taba faduwa jarrabawa ba.
"Kazalika ban samu kalubale daga wajen maigidana na farko da ya rasu ba da kuma maigidana na biyu da na sake aurensa. Duk sun bani goyon baya shi ya sa ma wahalhaluna ba su yi yawa ba.
"Kuma duk da irin hidimomin aiki a haka na samu lokacin yi wa yarana shida tarbiyya, kuma Alhamdulillahi ga su nan duk sun girma sun zama cikakkun mutane."
Sai dai mai shari'ar ta ce akwai lokacin da ta tafi hutun haihuwa bayan ta dawo ya kamata a kara mata girma zuwa alkalin babbar kotun jihar Bauchi, amma sai aka bai wa wani na kasa da ita.
"Sai daga baya nake ji ana cewa ashe a lokacin arewa ba ta shirya samun alkali mace ba shi ya sa aka yi min haka."
Wannan bayani ya amsa tambayar dumbin masu sauraro da suka hada da Usman Uba.
Shin an mata alfarma ne kafin ta samu wannan mukami?
Justice Bulkachuwa ta ce kamar yadda yake a tsarin aiki komai ana binsa ne daki-daki don haka babu wata alfarma da aka yi mata.
"Yadda ka zo haka za ka yi ta bin layi har abu ya zo kanka. Akwai matakai da yawa da ake bi don tantance ka kuma duk sai da na bi su.
Tallafawa sauran mata
"A fannin aikina dai na zama uwa don ko yaushe cikin gyara nake musamman mata masu tasowa da ke aikin lauya. Ina sa ido sosai don gyara a tarbiyyarsu da kuma aikinsu," in ji mai shari'a Bulkachuwa.
"Ina kuma taimakawa yara mara sa galihu zuwa makaranta don su ma su amfana a nan gaba.
Akwai wata tambayar da masu sauraro suka aiko kan yadda take ganin ci gaban mata a Najeriya.
"Gaskiya an samu ci gaba sosai, misali a fannin shari'a mun samu mace ta farko da ta zama babbar mai shari'a ta kasa Justice Maryam Alooma. Sannan akwai bangarori daban da dama suka yi zarra."
Justice Bulkachuwa ta yi kira ga mata masu dtasowa da su mayar da hankali wajen neman ilimi mai inganci su kuma rage buri na kyale-kyalen rayuwa.
"Ya kamata yaranmu masu tasowa su sani cewa dole su jajirce wajen inganta rayuwarsu da ta 'ya'yansu da ta jikokinsu masu zuwa, duba da halin da ake sake shiga a rayuwa."
Cin hanci
Masu sauraronmu da dama sun yi batun ko Justice Bulkachuwa na amince wa da karbar cin hanci da rashawa?
Amma a tattaunawarmu ta ce: "Alkwari na dauka fa tare da yin rantsuwa cewa ba zan cuci kasata da al'ummarta ba, to me zai sa na yi wani abu mara kyau?"
Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu suke mata kallon mace mai tsauri kuma mara son wargi, musamman yayin da take kotu.
Justice Bulkachuwa ta samu sunan Bulkachuwa ne daga mijinta na yanzu wani toshon dan siyasa a jihar Bauchi, Alhaji Adamu Bulkachuwa, wanda ta aura bayan mutuwar mijinta na farko.
Tana da 'ya'ya shida daga aure biyun da ta taba yi a rayuwarta. Kuma a cikin zuri'arsu mai matukar yawa, an fi kiranta ne da 'Adda Zainabu' don ganin cewa ita ce babba.