Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Auren wuri haramun ne - Save the Children
Wata gidauniyar tallafa wa kananan yara ta fada a cikin wani sabon rahoto cewa 'yan mata kimanin miliyan bakwai da rabi ake yi wa aure ba bisa ka'ida ba duk shekara.
A cewarta ana aurar da 'yan mata, suna kasa da shekaru mafi karanci da dokokin kasashensu suka kayyade.
Kungiyar Save the Children ta ce ana yin kashi 1 cikin 4 na duk auren da ta ce haramtattu ne a yankin yammaci da kuma Afirka ta tsakiya, inda ake tilasta wa yarinya 'yar shekara 12 yin aure a Senegal da kuma 'yar shekara 15 a Saliyo.
Sau da yawa yaran kan fito ne daga gidan da daya daga cikin mahaifa ya mutu, kuma suna da yiwuwar samun juna biyu da kuma aske makaranta.
Kungiyar ta bukaci illahirin kasashe su sanya shekara 18 ta zama mafi karancin shekarar aure ga 'ya mace.