Auren wuri haramun ne - Save the Children

Malagasy girl Imasy Lavorary poses with her daughter in Antananarivo, Madagascar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata karamar yarinya da aka yi wa aure tana goye da jaririnta

Wata gidauniyar tallafa wa kananan yara ta fada a cikin wani sabon rahoto cewa 'yan mata kimanin miliyan bakwai da rabi ake yi wa aure ba bisa ka'ida ba duk shekara.

A cewarta ana aurar da 'yan mata, suna kasa da shekaru mafi karanci da dokokin kasashensu suka kayyade.

Kungiyar Save the Children ta ce ana yin kashi 1 cikin 4 na duk auren da ta ce haramtattu ne a yankin yammaci da kuma Afirka ta tsakiya, inda ake tilasta wa yarinya 'yar shekara 12 yin aure a Senegal da kuma 'yar shekara 15 a Saliyo.

Njaka Ikandrina holding her child in her arms

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Njaka Ikandrina karamar amarya daga Madagascar tana dauke da danta

Sau da yawa yaran kan fito ne daga gidan da daya daga cikin mahaifa ya mutu, kuma suna da yiwuwar samun juna biyu da kuma aske makaranta.

Kungiyar ta bukaci illahirin kasashe su sanya shekara 18 ta zama mafi karancin shekarar aure ga 'ya mace.