Nigeria @ 57: 'Ba haka aka so ba!'

Flag of Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Wani masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, Dokta Abubakar Kari ya ce duk da sauye-sauyen da kasar ta samu a tsawon shekara 57, amma ta gaza ta fuskar nasarorinta bayan samun 'yancin kai.

Masanin siyasar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC.

"Irin fatan da ake da shi a shekarar 1960 na cewa an haifi sabuwar kasa wadda za ta kasance jagorar kasashen bakaken fata, kuma ta zama daya daga cikin manyan kasashen duniya, hakan bai samu ba."

Musammam idan aka yi la'akari da tarin albarkatun da Allah Ya hore mata, kamar yadda ya ce.

A ranar Lahadin ne Najeriya take bikin cika shekara 57 bayan ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1960.

Duk da haka Dokta Kari ya ce ba adalci ba ne a ce ba a samu ci gaban a-zo-a-gani ba a tsawon shekara 57 da samun 'yancin kasar.

"Misali, a 1960, a fannin ilimi a arewa, makarantun sakandare nawa muke da su? Mai yiwuwa ba su fi ashirin ba, amma yanzu muna da dubbai."

A cewarsa a yanzu hanyoyin mota sun karade Najeriya gaba daya, sannan akwai filayen jiragen sama da na ruwa.

"Akwai bunkasar al'umma. Wadannan duka ci gaba ne!"

Ya ce abin da ya sa mutane ke ganin kamar ba a samu ci gaba a Najeriya ba, shi ne tarin matsaloli wadanda ke tafiya da ci gaban.

Map of Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Dokta Kari ya ce matsalar Najeriya, idan an bi ta barawo to a bi ta ma bi sawu.

"Mu talakawa, wadanda ake mulka, muna ba da dama ga shugabanni su yi ta kawo mana rarrabuwar kai.

Su yi amfani da kabilanci da addini da bangarenci da sashe, su yi amfani da kudi da karya. Mutum yana gani, wannan mutum ba na kirki ba ne amma duk da haka ya zabe shi."

Ya ce hayaniyar neman raba kasar da Najeriya ke fuskanta a yanzu, ba sabon abu ba ne.

"Kusan za a ce bayan kowacce shekara goma ko ashirin sai an samu irin wannan hayaniyar.

Kamar yayi ne! Duk lokacin da wani bangare yake da wata bukata ko kuma ba a biya masa wata bukata ba, sai a fito a yi ta rudu kamar sama da kasa za ta hade."

Ya ce ya yi imani 'yan siyasa da 'yan bokon kasar sannu a hankali za su iya warware abinsu.

Malamin kimiyyar siyasar ya nanata bukatar yin adalci daga bangaren shugabanni.

A cewarsa: "Ina ganin duk abubuwan da suka janyo wadannan rigingimun tun farko shi ne rashin samun nasarar a-zo-a-gani wajen sarrafa dumbin albarkatun da Allah ya hore wa Najeriya."