Saudiyya na shan yabo kan 'yancin tukin mata

Wata mata 'yar Saudiyya a mota

Asalin hoton, Hannan Muhammad

Bayanan hoto, Da wannan doka ta Saudiyya a yanzu babu sauran wata kasa a duniya da mata ba sa tuka mota

Wannan mataki da Sarki Salman na Saudiyyar ya dauka ya sa masu fafutuka a kan hakan da sauran 'yancin mata a kasar murna ta baki har kunne, ganin hakarsu ta fara cimma ruwa.

Bugu da kari matakin ya jawo wa kasar yabo hatta daga babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres., da kuma Amurka, wadda Shugabanta Donbald Trump ya yaba a kai tare da yin alkawarin cigaba da dafa wa kasar don cimma burinta a wasu fannonin.

Mista Trump ya ce hakan kyakkyawan mataki ne na tabbatar da 'yancin mata da ba su dama a kasar ta Saudiyya.

Shugaban ya ce za su ci gaba da tallafa wa kasar a kokarinta na karfafa al'ummarta da bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar irin wadannan sauye-sauye da kuma aiwatar da gagarumin shirin raya kasar na shekara ta 2030 mai lakabin Saudi Vision 2030.

Jakadan Saudiyyar a Amurka Khaled Bin Salman, ya ce wannan babbar rana ce ta tarihi, kuma mataki ne da ya kamata wanda aka yi a lokacin da ya dace

Jakadan ya ma tabbatar cewa ba wai sai mace ta samu izinin wani muharraminta ba kafin ta dauki darasin koyon tukin, kuma tana da damar tuka motar a ko ina take so a kasar.

Mai fafutukar neman 'yancin matan na tuki a Saudiyyar, mai kamfe din da ake wa take da Women2Drive, Manal al-Sharif, wadda aka daure a kan keta dokar tukin da ta yi, ta fada a shafin twitter cewa; Saudi Arabia ta kama hanyar sauyi, kasar ba za ta taba zama kamar da ba.

Wata Mata

Asalin hoton, Getty Images

Yanzu dai bayan wannan sanarwa ta bayar da damar tukin ga mata, ma'aikatun gwamnatin Saudiyyar za su shirya rahoto cikin kwana 30, sannan za a aiwatar da dokar zuwa watan Yuni na shekara mai zuwa ta 2018.

Kasar Saudiyya dai ita kadai ce a duk duniya da ta hana mata tuka mota.

Yanzu ana iya cewa hankali ya kwanta a fannin wannan fafutuka, amma kuma wasu na ganin ta bude kofar neman wasu 'yancin na mata da sauransu.

Kungiyoyin kare 'yancin dan Adam sun shafe shekaru suna kiraye-kirayen ba mata damar tuki da kansu a kasar.

Kuma hukumomi sun sha tsare matan da suka karya dokar haramcin tukin mota.

Wata mata na murnar ba su damar tuka mota a Saudiyya

Asalin hoton, Hannan Muhammad

Bayanan hoto, Wasu mata na ta bidire da birede a kan ba su wannan 'yanci na tuka mota