America ta hana 'yan Chadi shiga kasarta

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Donald Trump na sanya sabon tarnakin shiga Amurka a kan kasa takwas ciki har da a karon farko Chadi da Koriya Ta Arewa da Venezuela.
Haramcin ya biyo bayan bitar harkokin tsaro da kuma nasarar da umarninsa na ainihi wanda wa'adinsa zai kare ya cim ma.
Shugaba Trump ya ce yana ba da fifiko wajen mayar da Amurka, kasa mai aminci.

Asalin hoton, Reuters
Tasirin dokokin dai ya sha bamban daga wannan kasa zuwa waccan, inda suke haramta wa 'yan Syria da Koriya Ta Arewa shiga Amurka kwata-kwata, amma suka yi tarnaki ga jami'an gwamnatin Venezuela.
A yanzu dai Sudan ba ta cikin jerin kasa shida na akasari musulmai da ke cikin haramcin Trump na farko.
Karo na uku kenan ana sabunta haramcin wanda ke shan mujadala a gaban kotu.







