Haushin kare kawai Trump yake yi - Koriya Ta Arewa

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Babban jami'in diflomasiyya na Koriya ta Arewa ya ce jawabin da Shugaba Donald Trump ya yi a Majalisar Dinkin Duniya, ''haushin kare ne.''
Da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba, Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, zai lalata Koriya ta Arewa gaba ɗaya idan ta zame wa Amurka ko kawayenta barazana.
Maganganun da Ministan Harkokin Wajen Koriya Ta Arewan Ri Yong-ho ya yi, sune kalamai na farko kan mayar da martani ga jawabin Trump.
Koriya ta Arewa ta ci gaba da shirye-shiryen makaman nukiliyarta duk kuwa da haramcin hakan da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata.
Mista Ri ya fadawa manema labarai a kusa da hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a New York cewa, ''Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru aa shaho sai ya yi."
Idan [Trump] yana tunani cewa zai iya ba mu mamaki da balokokon da yake yi ne, to lallai gara ya san cewa mafarki yake yi.
Da yake magana game da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un, Mista Trump ya fadawa Majalisar Dinkin Duniya cewa, ''Mai makaman roka yana son yin kunar bakin wake ne."
Lokacin da aka tambaye shi abin da yake tunani game da kiran Kim Jung-un da 'mai makaman roka,' sai Mr Ri ya ce: "Ina jin tausayin mataimakansa."
Mista Ri ya shirya ba da jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a.
Haka kuma a ranar Alhamis, Koriya ta Kudu ta ce za ta aika sabon taimakon jin kai ga Koriya Ta Arewa a karo na farko a kusan shekara biyu.
Maikatar hadin kai a Seoul na shirin samar da dala miliyan takwas ta hanyar shirin Majalisar Dinkin Duniya don taimakon yara da mata masu ciki da kuma da inganta kayayyakin kiwon lafiya.
Wannan mataki ya zo kwanaki bayan Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sabbin takunkumai a kan Pyongyang, na hana shiga da fitar da man fetur da kayayyaki - wani yunkuri na sanya Koriya Ta Arewa cikin halin yunwa.
Takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne a matsayin martani kan gwajin nukiliyar da Arewata yi a ranar 3 ga watan Satumba.
Masana sun ce Koriya ta Arewa ta yi matukar ci gaba da a kera makamai masu linzami da makaman nukiliya.















