Macen da ta fi kudi a duniya ta mutu tana da shekara 94

Liliane Bettencourt

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ms Bettencourt ita ce ta 14 a mutanen da suka fi kudi a duniya, bisa kididdigar da mujallar Forbes ta yi a shekarar 2017

Matar nan mai kamfanin kayan kwalliya na L'Oreal, Liliane Bettencourt, ta mutu tana da shekara 94 a duniya, in ji iyalanta.

Wata sanarwa ta ce ta mutu ne a gidanta da daddare.

Ita ce matar da ta fi sauran mata kudi a duniya inda take dakusan (£30bn; $40bn) a kiyasin da aka yi a shekarar 2017.

Ta bar shugabancin kamfanin a shekarar 2012 kuma ba kasafai ake ganinta a bainar jama'a ba tun daga wancan lokacin, ko da yake an yi ta labari a kanta saboda cutar mantuwar da ta yi fama da ita.

Sanarwar da shugaban kamfanin Jean-Paul Agon ya fitar ta ce: "Muna matukar kaunar Liliane Bettencourt wacce a ko da yaushe take kula da kamfanin L'Oreal da ma'aikatansa kuma take matukar son ganin kamfanin ya yi zarra.

"Ta taimakawa sosai wajen ganin kamfanin ya ci gaba. Ita mace ce mai kyawu wacce ba za a bata mantawa da ita ba."

Liliane Bettencourt ta bata da 'yarta Francoise Bettencourt-Meyers a shekarar 2007 lamarin da ya ja hankalin duniya.

Ms Bettencourt-Meyers ta kai karar mahaifiyarta a kotu ne inda ta yi zargin cewa hadimanta suna cutarta saboda sun ga ba ta da koshin lafiya.

An ba da rahoton cewa wani mai daukar hoto da ya zama abokin François-Marie Banier a shekarar 2008 t ya samu kyauta wasu kayayyaki daga wurinta wadanda suka kai miliyoyin daloli - cikinsu har da wasu zane-zane da Picasso ya yi da kuma kuma fili mai fadin eka 670 a tsibirin Seychelles.

Ms Bettencourt-Meyers tace ta kai karar Mr Banier bayan wata ma'aikaciyar mahaifiyarta ta shaida mata cewa mahaifiyar tata na shirin mayar da shi danta na riko.

Liliane Bettencourt and her daughter Francoise Bettencourt Meyers pictured in 2011

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hoton Ms Bettencourt da 'yarta da aka dauka a L'Oreal a shekarar 2011