Za a fara koyar da ilimin jihadi a makarantun Turkiyya

Makarantun Turkiyya sun fara sabuwar shekarar karatu ta bana cike da takaddama sakamakon gabatar da sabuwar manhajar karatu mai cike da ce-ce-ku-ce, wacce aka cire koyar da ilimin cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba zuwa mutum wato (Evolution), inda a madadin sa aka gabatar da ilimin jihadi.

A ganin gwamnati mai kishin Islama ta Turkiyya, an yi hakan ne domin sabbin dabi'un ilimi.

Masu suka sun yi tir da sabbin littatafan makarantun a matsayin masu wariya kan jinsi da kuma masu adawa da kimiyya, sun kuma sun yi korafi cewa hakan koma baya ne ga tsarin ilimin da ba ruwansa da addini.

Dan jam'iyyar hamayya ta CHP, Bulent Tezcan ya ce: "Suna kokarin gurbata tunanin yara ne ta hanyar saka karatun jihadi (a manhajar karatun yara) tare da irin fahimtar da ta tsunduma Gabas Ta Tsakiya cikin kashe-kashe."

Amman gwamnatin kasar ta soki 'yan hamayya da kokarin yada bakar farfaganda a wani yunkuri na raba al'ummar Turkiyya gabannin zabukan shekara 2019.

"Idan muka ce dabi'u, suna fahimtar wani abu ne daban. Muna alfahari da ra'ayinmu na 'yan mazan jiya masu bin tafarkin dimokradiyya, amman ba ma son kowa ya zama kamar mu," in ji ministan ilimi Ismet Yilmaz.

Kwato jihadi daga masu jihadi

Ana bayar da littattafan da ke bayanai kan jihadi a makarantun koyon sana'a na Turkiyyya, wadanda aka fi sani da sunan makarantun Imam-Hatip. Daga nan kuma za bai wa 'yan makarantar sakandare zabin darasin nan da shekara daya.

An ware wani littafi mai suna 'Rayuwar Annabi Muhammad (SAW)' domin yin tsokaci akai, kan zargin cewa an tabo batun wariyar jinsi da kuma bayanin kan jihadi da ya yi.

Kamus din cibiyar koyar da harshen Turkiyya ya bayyana jihadi a matsayin "yakin addini." Amman jami'an ma'aikatar ilimi sun ce kungiyoyin da ke ikirarin jihadi irin IS mai da'awar kafa daular Musulunci suna bata ma'anar jihadi domin cimma wasu bukatunsu.

Ministan ilimin ya ce ya kamata a shigo da sunan jihadi a matsayin wani bangare na addinin Islama a mahangar "kaunar kasa".

Ministan ya ce: "Jihadi wani bangare ne na addininmu. Nauyin da ya rataya a kanmu shi ne mu koyar da ko wanne abu ta yadda ya kamata tare da gyara abubuwan da aka yi wa mummunar fahimta".

Har wa yau littafin mai cike da ce-ce-ku-ce ya bayyana cewar mace ta yi wa mijinta "biyayya" wani nau'i ne na "ibada".

Amman jami'an gwamnati sun ce wannan ba abun mamaki ba ne tun da littafi ne na addinin Islama kuma ya ambato ayoyi daga Alkur'ani.

"Allah ne ya fada, ba ni ba. In yi masa gyara ne, ko mene ne?" in ji Alpaslan Durmus, wanda yake shugabantar hukumar ilimi.

Amma an gudanar da manyan zanga-zanga biyu a karshen makon da ya gabata, inda maudu'an #NoToSexistCurriculum da #SayNoToNonScientificCurriculum da kuma #DefendSecularEducation suka yi ta jan hankulan mutane a shafukan sada zumunta a Turkiyya.

Wani shugaban wata kungiya ya yi kira ga masu zanga-zanga su ce"tir da sabuwar manhajar da ta hana kimiyya a karni na 21".

'Yan hamayya sun zargi jam'iyyar AKP mai mulki ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan da maye gurbin ginshikin jamhuriyar Turkiyya mara addini da dabi'un Islama da na masu tsattsaruran ra'ayi.

Kalaman da suhgaban kasar ya furta kan samar da wata al'umma saliha sun janyo fargaba a zukatan wasu.

Ma'akatar ilimin ta kuma ce masu suka "jahilai ne" domin sun yi da'awar cewar an cire ilimin cewa halittar dan adam ta sauya ne daga dabba zuwa mutum wato (evolution) gabadaya daga manhajar karatu.

Ministan ya ce za a karantar da wasu sassa na ilimin rikidar halittar (evolution) a matakin sakandare, amma ba da sunan na evolution ba.

Amman Aysel Madra daga cibiyar garambawul ga Ilimi a Turkiyya na ganin yin hakan zai rudar da yara ne kawai.

Kawunan kungiyoyin malamai ma sun rabu kan muhawarar jihadi.