'Dan autan' mawakan hip hop na Hausa Lil Ameer ya rasu

Asalin hoton, LIL AMEER/ FACEBOOK
Lil Ameer, wanda ake yi wa lakabi da dan autan mawakan hip hop na Hausa ya rasu.
Mawakin, wanda ya yi fice a jihar Kano da wasu yankunan arewacin Najeriya, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota yana da shekara 14 a duniya.
Lil Amir ya yi wakoki da dama kuma masana harkokin fina-finan Kannywood irin su Farfesa Abdallah Uba Adamu sun sha yin sharhi kan wakokinsa.
Dan autan mawakan yana da kyakkyawar alaka da fitaccen jarumin fina-finan na Kannywood Adam Zango wanda ke yawan yabonsa.

Asalin hoton, FACEBOOK/ADAM ZANGO
A sakon ta'aziyyar da ya wallafa a shafinsu na Instagram, Adam Zango ya yi addu'ar cewa "Allah ya jikanka karamin dan uwana. Allah ya sa Aljanna makoma. Kai duniya ba a bakin komai take ba!"
Sauran fitattun jarumai da masana harkokin fina-finan Kannywood irinsu Ali Nuhu da Ibrahim Sheme da makamantansu sun yi addu'ar Allah ya gafarta Lil Amir.
Fitattun wakokin da marigayin ya rera sun hada da "Kai Matsa Mana", "Dance for me", da sauransu.

Asalin hoton, LIL AMEER/ FACEBOOK






