Nigeria: Har yanzu ba a biya likitocin da suka yi yaki da Ebola ba

A health official waits to screen for the Ebola virus Muslim faithfuls on pilgrimage to Mecca on September 19, 2014 at the Murtala Mohammed International Airport in Lagos.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tantance masu dauke da cutar Ebola a iyakokin Najeriya sun taimaka wajen dakile bazuwar ta

A cikin jerin wasikunmu na 'yan jaridar Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani, ta yi duba kan korafe-korafen ma'aikatan lafiyar da suka ceto Najeriya daga fadawa cikin bala'in annobar Ebola a shekarar 2014, wadanda suka yi aiki tukuru amma har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba.

A watan Oktobar 2014 ne Najeriya ta samu yabo a duniya kan yadda ta yi gaggawar dakile yaduwar annobar cutar Ebola, wadda ta yi barna sosai a makwabtanta da ke Yammacin Afirka kamar su Saliyo da Guinea da Laberiya.

Amma tuni likitocin babbar tawagar da suka yi wannan hobbasa na Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, suka bar aikinsu, saboda an ki biyansu albashinsu na kusan shekara uku.

"Idan da za su iya dawo da hannun agogo baya, ba za su neme ni don na yi aikin nan ba," in ji Dr Kenneth Madiebo, wani likita mai shekara 53 da ya kula da gawar Patrick Sawyer, wanda shi ne mutum na farko da aka gano yana dauke da cutar Ebola a Najeriya a shekarar 2014.

Dr Madiebo wanda jami'i ne a cibiyar NCDC tun watan Satumbar 2012, an sanya shi aikin kawar da duk wani abu da zai iya yada cutar daga dakin asibitin da Mista Sawyer ya mutu a watan Yulin 2014, kuma shi ne ya kintsa gawar mamacin don a konata.

A wani bidiyo da ya nuna min, Dr Madiebo, wanda shi ne kadai jami'in lafiyar da ya yi wannan hobbasa, ya jagoranci masu kula da gawa wajen ciro gawar Mista Sawyer daga wani da tsukukun ban-daki inda a nan ne ya mutu.

Sitting by the coffin used to evacuate Patrick Sawyer

Asalin hoton, Kenneth Madiebo

Bayanan hoto, Likita Madiebo tare da ma'aikatan da suka kula da gawar Patrick Sawyer

A tabbatar da mutuwar Mista Sawyer tun karfe 7:30 na safe amma ba a ciro gawarsa ba sai karfe 11:30 na dare.

Dr Madiebo ya ce: "Kowa yana jin tsoro, ba wanda yake son yin wannan aiki. Amma ni na yi saboda aikina ne."

"Na yi rashin lafiya kwanaki kadan bayan hakan, amma na san firgici ne kawai ba Ebola ba."

Ya samu yabo daga wajen mutane a yayin da aka sanar a hukumance cewa babu Ebola a Najeriya a ranar 20 ga watan Oktoba, bayan nan kuma ministan lafiyar kasar a wancan lokaci Onyebuchi Chukwu, ya umarci Dr Madiebo ya mike tsaye a yayin wani taron manema labarai, inda ya jinjina masa tare da yabonsa a gaban mutane kan rawar da ya taka ta dakile yaduwar Ebola.

A wannan watan ne kuma dai ministan ya yi murabus daga mukaminsa don tsayawa takarar siyasa, a yayin da shi kuma Dr Madiebo ya samu ci gaba a aikinsa, matsayin da ya sa yawan albashinsa ya karu.

Amma fa tun daga wancan lokacin har zuwa yau ba a sake biyansa albashi ba, walau sabon ko tsohon.

Wata abokiyar aikinsa Colette Isu-Ezumah, mai shekara 43, wadda ta koma Najeriya daga Amurka a shekarar 2011, ta bani labarin irin wannan tagayyara.

Ita ce kashin bayan hada wannan tawagar ta masu aikin sa-kai 'yan Najeriya 250 da aka tura Saliyo da Laberiya domin su taimaka wajen yaki da Ebola, a yayin da cutar ke kan ganiyar yaduwarta a shekarar 2014 da 2015.

Baya ga wannan, kuma dai kamar yadda ya faru ga Dr Madiebo, ita ma Ms Isu-Ezumahba a biyata albashi ba tu watan Oktobar 2014.

"Shugabanmu ya sha gaya mana cewa ka da mu damu, za a biya mu,: in ji ta.

line

Annobar Ebola a 2014:

Health workers from the Sierra Leone's Red Cross Society Burial Team 7 place a body in a grave at King Tom cemetary in Freetown on November 12, 2014

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Annobar Ebola wacce tayi sanadiyyar mutuwar mutum 11,000 ta kuskure Najeriya
  • Ita ce annoba mafi muni a tarihi
  • Fiye da mutum 11,000 ne suka mutu - yawancinsu a Saliyo da Laberiya da Guinea
  • An samu wasu mace-macen a Najeriya da Mali da Amurka
  • Ta faro ne a Guinea a watan Disambar 2013, ta zo karshe a watan Janairun 2016
line

Da ya gaji da gafara sa bai ga kaho ba, sai kawai Dr Madiebo ya dauki hukunci a hannunsa.

A wannan lokaci ba a dade da zabar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar ba, kuma da yake ba a saka sabon minista a ma'aikatar lafiya ba, sai babban sakatare Linus Awute ya zama shi ke jan ragamar.

Dr Madiebo ya aikawa Mr Awute sakon email, tare da sanya sunan abokan aikinsa shida wadanda su ma ba a biya su albashi ba tsawon wata tara.

Amma a amsar da Mr Awute ya aikawa Dr Madiebo sai ya ce: "Baka da damar da za ka turo min sakon email kai tsaye, bayan ka san cewa kana aiki ne karkashin mutane da dama a ma'aikatar lafiya ta kasa."

"Ina wannan hali na rashin da'a da rashin ladabi ya samo asali?"

Teachers of Tundunwada Secondary School speak to students about Ebola during an assembly in Abuja on September 22, 2014.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An bai wa mutane da dama wadanda suka hada da 'yan makaranta shawarar irin matakan kariyar da ya kamata su dauka

Ya kara da cewa: "A iyakar sanina, tsarin biyan albashinka yana karkshin wata doka ce ta ma'aikatar lafiya ta kasa.

"Kuskure daya a nan shi ne ma'aikatar lafiya na bukatar dakatar da kai na dan wani lokaci saboda wannan sakon email din naka mai cike da rudani.

'A nuna adalci'

Sai dai kalaman karshe na email din Mr Awute sun sa masa kwarin gwiwa:

"Bayan tauttaunawar da na yi da sashen da ka ke aiki karkashinsa, na yanke shawarar neman hanyar da za a maida ka cikin ma'aikatan gwamnati".

Da suka samu wannan kwarin gwiwa ne sai Dr Madiebo da abokan aikinsa suka ci gaba da aikinsu.

A poster reading 'Ebola Sickness' is displayed at the main entrance of Nigerian Health Minister's office in Abuja on August 6, 2014.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan sakon na Ingilishin buroka an rika amfani da shi ne wajen fadakar da jama'a a shekarar 2014

Daya daga cikin likitocin da suka assasa cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC a watan Satumbar 2012, Dr Chuks Ukpaka, ya ce: "Na bar aikina a Birtaniya don na zo kasata na taimaka wajen gyaruwar bangaren lafiya da ya lalace ta hanyar amfani da kwarewata ta shekara 15.

"Ba a taba dakatar da mu daga aiki ba, amma dai an yi mana alkawarin biyanmu albashinmu da muke bi."

Abin da ke gaban Dokta Madiebo shi ne hada wani shirin kula da wadanda suka yi aiki da masu fama da cutar Ebola na mako uku.

Daga baya kuma wani aiki mafi hatsari ya biyo wannan, inda ya dauki jinin wanda ake tsammanin yana dauke da cutar Lassa a wani asibiti da ke birnin Abuja a shekarar 2016.

"Kowa ya dauka bani da hankali ne," in ji shi. "Har ma'aikatan sashen bincike ma na tsoron karbar samfurin jinin da na debo".

Muna neman adalci

Duk da haka ba a biya su albashinsu ba.

Saboda haka sai Likita Madiebo ya cigaba da rubuta wa Mista Awute da sauran manyan jami'an ma'aikatar lafiya wasiku tuni, kuma yana ganin wannan ne dalilin da yasa suke kallonsa a matsayin dan rigima.

Lokacin da hukumar NCDC ta koma sabon gininta a shekarar 2015, Likita Madiebo ya fuskanci wariya, inda aka ki ba shi ofishin da zai rika gudanar da aiki:

"Daga baya sai na daina zuwa wajen aiki saboda sun ki bani ofis don ka da su biyani".

line

Adaobi Tricia Nwaubani:

Adaobi Tricia Nwaubani

Asalin hoton, Adaobi Tricia Nwaubani

Najeriya ta yi asarar kwarewar ayarin jami'an da suka taimaka ta yaki cutar Ebola

line

Shugaban hukumar NCDC daga shekarar 2011 zuwa ta 2016, Abdul Nasidi, ya tabbatar da cewa ba a biya albashin ma'aikatan ba, amma ya ce ba laifinsa ba ne: "Nima ba a biya ni wani bangaren albashina ba".

Amma da alama kokarin Likita Madiebo na aikawa da sakon imel dangane da rashin biyan albashinsu ya kusa cimma nasara, bayan da Ministan Kiwon Lafiya na Najeriya, Isaac Adewole, ya fitar da wata sanarwa a watan Mayun 2017 da zummar duba lamarin.

"Ma'aikatar Lafiya na son ganin an yi wa wadannan mutanen adalci", in ji Halad Keana, jami'in da ke jagorantar ayyukan gyaran tsarin aiki da ake wa ma'aikatar.

Ya kuma kara da cewa za a tura wa minista Adewole lafiya sakamakon aikin nasu bayan kwamitin nasu ya kammala zama a karshen watan Satumba.

Amma Najeriya ta yi asarar kwarewar ayarin jami'an da suka taimaka ta yi nasarar yaki da cutar Ebola, kuma ba makawa dole ta sake sabon shiri idan ta sake fuskantar irin wannan annobar.

A pharmacist searches for drugs in a pharmacy in Lagos on July 26, 2014. Nigeria was on alert against the possible spread of Ebola on July 26, a day after the first confirmed death from the virus in Lagos.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kamfanonin hada magunguna na kokarin samar da wani rigakafin kamuwa daga cutar ta Ebola

"Na kasa biyan kudin hayar gidana, da kudin makarantar 'ya'yana har da kudin motar zuwa wurin aiki," in ji Ms Isu-Ezumah.

"A yayin da aka kwantar da dana a asibiti a watan Maris na 2016, kuma na kasa biya masa kudin magani, na yi tunanin cewa da na yi zamana a Amurka da ban fuskanci irin wannan matsalar ba".

Ta bar Najeriya a watan Yulin 2016, kuma a yanzu tana aiki tare da ma'aikatar lafiya ta Amurka.

Likita Ukpaka ma ya koma Ingila, inda yake aiki a matsayin mai koyar da jami'an kiwon lafiya da kuma babban likita. Amma ya ce har yanzu hankalinsa na gida Najeriya, duk da matsalolin da ya fuskanta a hannun hukumar NCDC:

"Akwai kalubale masu yawa a bangaren kiwon lafiya da suke bukatar kwarewata."

Har yanzu likita Madiebo na daukar kansa a matsayin ma'aikacin NCDC domin kawo yanzu babu wanda ya aika masa da takardar sallama.

"Sun tatse ni," in ji shi. "Da na sani da ban fara wannan aiki ba, da na yi wani aikin na dabam da yafi min".