Alhazan Nigeria bakwai sun mutu a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Wasu alhazan Najeriya bakwai sun mutu a Saudiyya gabanin a fara aikin Hajji.
Alhazan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna.
Sannan wata Hajiya daga Jihar Kogi ta Haihu a Madina. Shugaban NAHCON Abdullahi Mukhtar, ya ce za a hukunta jihar da matar ta fito ta hanyar rage mata kujeru a badi, da kuma hukunta shugabannin hukumar aikin hajji ta jihar.
Alhazan Nigeria Kusan dabu 90 ne ke halartar aikin hajjin bana.







