Me zai faru idan Buhari bai dawo ba bayan kwana 90?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Umar Rayyan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Wasu 'yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan makomar kujerar Shugaban Kasar Muhammadu Buhari, wanda yake doguwar jinya a kasar Birtaniya, inda wasu suke cewa shugaban zai iya rasa kujerarsa idan bai koma gida ba bayan cikar kwana 90.
"Wai da gaske ne idan Shugaba Buhari ya yi kwana 90 bai dawo ba za a sauke shi, mataimakinsa ya hau?," in ji Mustapha Muhammad Mustey wanda ya bayyana ra'ayinsa a shafin BBC Hausa Facebook.
"Kwarai da gaske, domin haka kundin, tsarin mulkin Najeriya ya tanadar,"kamar yadda Abubakar Dan Azumi Bakori ya mayar wa Mustapha martani.
A karshen makonnnan ne shugaban zai cika kwana 90 yana jinya a wajen kasar, kuma kawo yanzu ba a bayyana cutar da take damunsa ba.
A bangare guda akwai masu ganin cewa "babu abin zai samu kujerar shugaban koda ko zai shekara ne a kasar waje don babu wata doka da ta ce a sauke shi."

Abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce
Barrister Muhammad Shuaib ya ce babu wani tanadin doka a Najeriya da ya ce shugaban kasa ya sauka daga mukaminsa idan ya kwashe wasu kwanaki yana jinya a kasashen ketare.
Ya ce dalilai biyar kawai ke sa shugaban kasa ya rasa kujerarsa, kamar yadda kudin tsarin mulkin kasar ya zayyana:
- Idan kotu ta soke zabensa
- Majalisa za ta iya tsige shi idan ya yi laifi
- Idan yana rashin lafiyar mai tsanani wanda zai hana shi ci gaba da shugabanci
- Mutuwa wato idan shugaban ba ya sauran lumfashi
- Ko kuma idan bisa radin kansa ya yi murabus

Lauyan ya ce bayan wadannan dalilai, babu wani sashi na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ce idan shugaba ya yi kwana 90 ko fiye da haka zai rasa kujerarsa.
Har ila yau, lauyan ya ce doka ta ba majalisa dama cewa idan shugaban kasa ya yi tafiya har tsawon kwana 21 ba tare da sanar da ita ba, to majalisa za ta yi kudiri wanda zai nada mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Asalin hoton, Twitter/@ProfOsinbajo
Hakazalika, akwai abin da ya faru shekarun baya a jihar Taraba inda Gwamna Danbaba Suntai ya yi mummunan hadari.
Abin da ya sa gwamnan yin doguwar jinya kafin rasuwarsa a watan Yunin bana.
Mataimakinsa Alhaji Umar Garba UTC ya ci gaba da shugabanci a matsayin mukaddashin gwamna har kusan shekara uku, amma ba tare da shi Gwamnan Suntai ya rasa kujerarsa ba.
Marigayi Suntai ya rasa kujerarsa ne bayan da wa'adinsa na shekara hudu ya cika wato bayan gudanar da zaben shekarar 2015.
A yanzu dai mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ne yake tafiyar da a'amuran kasar kuma ba a bayyana sanda Shugaba Buhari zai dawo ba.
Sai dai 'yan kwanakinnan shugaban ya gana da mataimakin nasa da kuma wasu gwamnonin kasar, abun da wasu ke ganin cewar alamu ne dake nuna cewar yana samun sauki.
Babu shakka dai, rashin lafiya shugaban da kuma ci gaba da zamansa a Landan ba zai ci gaba da jan hankalin 'yan kasar da kuma masu bibiyar al'amuranta.


Asalin hoton, Twitter/@MBuhari
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a Landan
23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnoni
26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu karin gwamnoni
Karanta karin labarai kan Buhari:











