An kama wani yariman Saudiyya kan cin zarafi

Asalin hoton, Reuters
An kama wani yariman Saudiyya kan zargin da aka yi masa na kasancewar hannunsa a wani lamarin cin zarafin dan adam da aka nada a faifan bidiyo.
Sarki Salman ya bayar da umurnin a kama shi nan take bayan bidiyon ya bayyana a Intanet kuma ya bazu, lamarin da ya sa ya zama abin da aka fi magana a kai a shafukan Intanet na kasashen Labarawa.
An kwarmata bidiyon kama matashin yariman, mai dogon bakin gashi da bakar riga a Intanet, inda aka yi ta yayatawa tare murna a kafofin sada zumunta na Saudiyya.
Umarnin sarkin ya tabbatar da cewar za a dauki matakai domin hana tilastawa tare da cin zarafin mutane komai matsayin mutum.
Karanta labarai masu alaka:






