Evans ya shigar da 'yan sandan Nigeria kara a Kotu

Asalin hoton, Idris facebook
Mutumin da ake zargin shi ne madugun satar mutane a Najeriya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya shigar da karar 'yan sanda a kotu.
Evans na zargin sufeton janar na 'yan sandan kasar, Ibrahim Idris da kuma wasu jami'an 'yan sanda uku a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lagos, inda yake zargin 'yan sandan da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Lauyan mutumin ne ya shigar da karar a madadin Evans, inda ya nemi kotu da sa wadanda yake karar su gurfanar da shi ba tare da bata lokaci ba.
Karar wadda aka shigar a makon jiya ta bukaci kotu ta sa 'yan sanda su tuhume shi idan suna zarginsa da wani laifi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
A farkon wannan watan na Yuni ne dai aka cafke Evans tare da wasu mutum shida da ake zarginsu da ayyukan satar mutane.
Kuma tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar nemansa ruwa a jallo.
Sai dai kakakin 'yan sanda, Jimoh Moshood ya shaida wa BBC cewa sun samu umarnin wata kotun tarayya wadda ta ba su damar tsare Evans har sai sun kammala bincike a kansu.
Rundunar 'yan sandan Ghana ma ta sanar da kaddamar da bincike a kan Evans din wanda ke da fasfo na kasar, haka kuma iyalinsa ma na zaune ne a Ghanan.











