'Yan matan Chibok 82 sun hadu da iyayensu

'Yan matan Chibok tamanin da biyu da kungiyar Boko Haram ta sako makonni biyu da suka wuce, sun hadu da iyayensu a karon farko tun bayan da aka sace su sama da shekaru uku da suka wuce.

'Yan matan sun yi rawa da murna yayin da iyayen na su ke saukowa daga kan motocin bus da suka kai su Abuja daga kauyen na Chibok dake jihar Borno.

Iyaye da 'yan uwan 'yan matan sun rika rungumesu, tare da zubar da hawaye na farin ciki.

Har yanzu, ana ci gaba da duba lafiyar 'yan matan, kafin bar su su koma gidajensu da kuma makaranta.

Gwamnatin Najeriyar dai na ci gaba da tattaunawa don ceto sauran 'yan matan sama da dari da har yanzu suke hannun kungiyar Boko Haram.