Hotunan Aishwarya Rai a bikin baje kolin fina-finai na Cannes

Asalin hoton, Image Smith PR
2002: Aishwarya Rai Bachchan, wadda ake yiwa kallon daya daga cikin mata mafi kyau a duniya, ta halarci bikin baje kolin fina-finai na Cannes a karon farko a shekarar 2002 a kan fim din Devdas.Sun je wannan biki ne tare da Shahrukh Khan da kuma Sanjay Leela Bhansali.

Asalin hoton, Image Smith PR
2003: A karon farko Aishwarya Rai Bachchan ta shiga cikin alkalan da za su zabi fim din da ya fi fice a bikin baje kolin fina-finai na Cannes.

Asalin hoton, Image Smith PR
2004: Aishwarya Rai da kawayanta

Asalin hoton, Image Smith PR
2005: Aishwarya ta yi shiga mai kyau inda ta saka farar doguwar riga mai ratsin fulawa.

Asalin hoton, Image Smith PR
2006: Aishwarya Rai Bachchan ta zama abar kwatance sakamakon shigar da ta yi a wajen bikin baje kolin fina-finai na Cannes.

Asalin hoton, Image Smith PR
2007:Aishwarya Rai Bachchan sun yi aure da Abhishek Bachchan a 2007, kuma wannan ne karon farko da su ka je bikin baje kolin fina-finai na Cannes tare da mijinta.

Asalin hoton, Image Smith PR
2008: Aishwarya ta samu iyalan Mr Bachchan a wajen bikin baje kolin fina-finai na Cannes. Amitabh Bachchan da Abhishek Bachchan, sun hadu da Aishwarya a bikin.

Asalin hoton, Image Smith PR
2009: Aishwarya Rai Bachchan ta sa ke halartar bikin baje kolin fina-finai na Cannes tare da mijinta Abhishek Bachchan.

Asalin hoton, Image Smith PR
2010: Aishwarya, wadda ta halarci bikin shekarar 2010 cikin bakar riga, ta tallata fim din Raavan a bikin.

Asalin hoton, Image Smith PR
2011: Aishwarya Rai Bachchan ta halarci bikin baje kolin fina-finan na 2011 ne a lokacin ta na da juna biyu.

Asalin hoton, Image Smith PR
2012: Aishwarya Rai Bachchan ta halarci taron baje kolin fina-finan a shekarar 2012 bayan ta haifi 'yarta Aaradhya, duk da ta kara kiba, kyawunta bai dusashe ba.

Asalin hoton, Image Smith PR
2013: Aishwarya ta halarci bikin na wannan shekara sanye da doguwar riga baka mai launi a jikinta.

Asalin hoton, Image Smith PR
2014: Aishwarya Rai Bachchan ta na dariya a lokacin da ta halarci bikin baje kolin shekarar 2014 sanye da doguwar riga mai launin ruwan gwal.

Asalin hoton, Image Smith PR
2015: Aishwarya Rai ta je bikin sanye da kyakkyawar doguwar riga.

Asalin hoton, Image Smith PR
2016: Aishwarya Rai Bachchan ta sha suka a kafafan sada zumunta saboda jan bakin da ta shafa a bikin baje kolin fina-finai na Cannes a bara. Amma a bikin na bana, ana jiran aga irin shigar da Aishwarya Rai zata yi a wajen bikin baje kolin fina-finai na Cannes.











