An daga mutum-mutumin Fir'auna a Masar

Asalin hoton, Empics
An daga wani katon mutum-mutumi na Fir'auna, wanda ake kyautata zaton ya yi shekara 3,000 daga karkashin kasa a Masar.
A makon da ya gabata ne dai aka dago wani katon kai da wasu sassan mutum-mutumin daga inda aka dago na Fir'aunan.
An gano shi ne a arewa maso gabashin birnin Alkahira a kusa da wurin bautar Ramses II, kuma masana sun yi amannar zai iya wakiltarsa.
An yi amfani da dutsen quarzite ne wajen sassaka mutum-mutumin.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar kayan tarihi ta ce za ta kai kuma ta hada bangarorin mutum-mutumin gidan adana kayan tarihi da ke tsakiyar birnin Alkahira, babban birnin kasar. Ta na fatan za a iya hade manyan bangarorin wuri guda.
Mazauna yankin, wadanda ke kusa da inda aka dago mutum-mutumin sun yi ta raha, daya daga cikin wadanda suka gano mutum-mutumin ya ce idan dai har ya kasance na ainihi ne, ba wai wanda aka sassaka ba, zai zamanto abu mai muhimmanci.
A makon da ya gabata ne dai kungiyar binciken ma'adinan tarihi ta gano mutum-mutumin mai nauyin ton 3, ana sa ran za a gama dago shi a wannan makon.







