Da gaske ƴan Najeriya na shiga aikin soja a Rasha?

Lokacin karatu: Minti 5

Tirka-tirka tsakanin ƙasashen Afirka da dama da Rasha kan ɗaukar wasu maza ƴan Afirka aikin soji don yaƙi a Ukraine na iya ƙara ruruwa bayan da jami'an Kyiv suka sanar da cewa an gano gawar wasu ƴan Najeriya biyu a yankin Donbas.

A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron ƙasar ta Ukraine ta fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairu, ta ce ta fitar da hotunan wasu ƴan Najeriya biyu da ake zargin sun mutu ne yayin da suke kare ƙasar Rasha.

Ma'aikatar ta ce an gano gawarwakin Hamzat Kazeem Kolawole da Mbah Stephen a Luhansk, kuma sun ce dukkansu biyu sun yi rajistar shiga rundunar sojin Rasha ne a shekarar 2025.

Kolawole, mai shekaru 42 da Udoka, mai shekaru 37, sun shiga rundunar sojan Rasha ta 423 na Guards Motor Rifle Regiment, na 4th Guards Kantemirovskaya Tank Regiment, ba tare da wani horon soji ba kuma aka tura su fagen daga, inji sojojin Ukraine.

"Udoka bai samu horo ba ko kaɗan - bayan kwanaki biyar kacal, a ranar 3 ga watan Oktoba, aka tura shi zuwa yankunan Ukraine da aka mamaye na wucin gadi.

"Babu abin da ke nuna Kolawole ya samu wani horo, mai yiwuwa bai samu horon soja ba. Matarsa da 'ƴaƴa uku suna Najeriya," in ji sanarwar.

Mutuwar tasu ta zo ne a daidai lokacin da damuwar ƙasashen Afirka da dama ke ƙaruwa game da adadin mutanen da aka ce ana ɗaukar su aiki don yi wa Rasha yaƙi.

Ko da yake BBC ba ta iya tabbatar da sahihancin wannan ikirarin ba, kuma gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wannan sabuwar sanarwar ba, amma wannan batu ya ƙara rura wutar damuwar da ake nunawa game da ɗaukar mayaƙa daga ƙasashen waje a yaƙin na Ukraine.

Moscow ta musanta ɗaukar ƴan Najeriya aikin soji

A farkon wannan makon nan ne jakadan Rasha a Najeriya Andrey Podyolyshev ya musanta cewa Moscow na daukar ƴan Najeriya aiki domin shiga cikin jerin mayaƙan da ke taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine.

Ya ce ba shi da masaniya kan duk wani shirin gwamnati na ɗaukar ƴan Najeriya aiki domin yaƙi a Ukraine, ya kuma ƙara da cewa idan har haka na faruwa, Rasha ba ta da hannu a ciki.

Sai dai sanarwar da rundunar sojin Ukraine ta fitar ta bayar da cikakken bayani kan ƴan Najeriya da suka mutu a fagen yaƙi da kuma yadda suka shiga rundunar sojin Rasha.

Hamzat Kolawole ya rattaba hannu kan kwantiragin shiga rundunar sojin ƙasar Rasha a watan Agustan 2025 sannan Mbah Udoka ya shuga rundunar ne a ranar 28 ga watan Satumban wannan shekarar.

Sanarwar ta ce ƴan Najeriyan guda biyu ba su samu horon soji ba kuma sun mutu a wani yunƙuri na kai farmaki kan yankunan Ukraine da ke yankin Luhansk. "Ba su samu damar yin wani artabu ba - kuma jirage marasa matuƙa ne suka kashe sojojin hayar".

A haɗe da bayanin, akwai hotunan wasu ƴan Najeriyan biyu da ke sanye da rigar sojoji, da wasu takardu guda uku da ke ba da ƙarin bayani kan sunayensu da kuma inda suka fito.

Ukraine ba bayyana yadda aka yi ta samu waɗannan takardun da ke nuna cikakkun bayanan kwantiragi da matsayin soja na sojojin biyu ba.

BBC ba ta iya tantance sahihancin takardun ko bayanan da ke ƙunshe a cikin su ba.

Ƴan Afirka fiye da 1000 sun shiga rundunar sojin Rasha tsakanin 2023 zuwa 2025 - Rahoto

Wani sabon bincike da aka wallafa rahotonsa a ranar 11 ga watan Fabrairu ya nuna cewa mayaƙan Afrika 1,417 ne aka ɗauka aikin sojan Rasha tun daga shekarar 2023, ciki har da 316 da aka tabbatar da mutuwarsu.

Rahoton da 'All Eyes On Wagner '(AEOW) ta wallafa ya ƙunshi jerin sunayen mayaƙa 1,417 daga ƙasashen Afirka 35 da suka shiga aiki a rundunar sojan ƙasar Rasha tsakanin shekarar 2023 zuwa tsakiyar 2025, daga cikin su 316 ne suka mutu.

Wani bincike da aka gudanar da kafar yaɗa labarai ta Faransa RFI ya ruwaito a ranar 11 ga watan Fabrairun da ya gabata ya nuna yadda ake ɗaukar mayaƙan Afirka domin taya Rasha yaƙi a Ukraine, ya kuma fitar da jerin sunayen waɗanda aka ɗauka - da waɗanda aka kashe - a fagen daga.

Yayin da Masar ke da mafi yawan ma'aikatan da aka ɗauka (361), Kamaru ta yi fi kowace ƙasa asara inda ƴan ƙasarta 94 ne suka mutu daga cikin 335 da aka gano.

Ƙasar Gambia ma ta yi asarar ƴan ƙasarta inda 23 daga cikin 56 da aka ɗauka aikin soja suka mutu.

Bayanan da aka samu ta hanyar shirin miƙa wuya na "I want to live" na Ukraine - ya nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai kashi 22 cikin 100, wanda bai haɗa da waɗanda suka jikkata ko suka ɓace ba.

Ƙiyasin gwamnatin Kenya ya ce kusan ƴan asalin ƙasarta 200 ne aka ɗauka aiki don yin yaƙi tare da Rasha.

Iyalai da yawa a faɗin Afirka sun ce sun kwashe tsawon watanni ba tare da sun ji ɗuriyar ƴanuwansu ba, in ji rahoton.

Lou Osborne na AEOW ya ce "Wallafa jerin sunayen ya bai wa iyalai damar… su san makomar ƴan uwansu, su tuntuɓi hukumomin ƙasa don neman a dawo da gawarwakin.

Wani rahoto na baya-bayan nan daga Cibiyar Hulɗar ƙasa da ƙasa ta Faransa (Ifri) ta ce ƴan Afirka 3,000 zuwa 4,000 ne ke cikin mayaƙa ƴan ƙasashen waje 18,000 zuwa 20,000 da ke aiki a Rasha, kamar yadda RFI ta ruwaito.

"Tun daga shekarar 2023, Rasha ta ƙara ƙaimi a yunƙurin da ta ke yi na ƙarfafa rundunar sojinta domin fuskantar yaƙin" in ji AEOW.

Sun ce da farko Moscow ta dogara ne kan fursunoni kafin ta karkata akalarta zuwa Afirka.

Masu bincike na IFRI sun ce yunƙurin ɗaukar ma'aikata yana harin matasa talakawa ne waɗanda ke ganin cirani a matsayin babbar dama ta barin ƙasa.

An yaudari da dama daga cikinsu da ayyukan yi na bogi ko kuma tayin karatu - lamarin da AEOW ya kasance tamkar fataucin mutane, inda ake amfani da waɗanda ake ɗauka a matsayin zakarun gwajin dafi a fagen yaƙi.

Masu bincike sun gano cewa cibiyoyin hadn gwiwa na masu shirya tafitye-tafiye da masu ɗaukar ma'aikata da ke aiki a cikin Rasha da Afirka, suna tallata "hanyoyi masu sauri" a Facebook, Instagram, Telegram da TikTok inda suke yaɗa hotunan motoci alfarma da kuma manyan gine-ginen birnin Moscow.

Tallace-tallacen suna yawan yin alƙawarin ɗaukar ma'aikata waɗanda ke sanya hannu kan kwantiragin da za a biya su albashin $2,000 zuwa $2,500 a kowane wata, da alawus, da inshorar lafiya da samun sauƙin zama ɗan ƙasa - alkawuran da yawancin mutane suka ce magana ce kawai ta fatar baki.

AEOW tana kuma da bayanan ɗaliban da aka tura daga zauren karatu zuwa fagen fama, ciki har da ɗan Senegal Malick Diop, wanda a yanzu yake garƙame a kurkuku a ƙasar Ukraine, da wani ɗan ƙasar Masar mai shekaru 25 da ya kammala karatun digiri, wanda ya ce sun tilasta masa sanya hannu kan kwangilar soja don a tsawaita masa bizarsa.

Kimanin ƴan Afirka 1,400 ne daga ko'ina cikin Afirka ke fafatawa tare da sojojin Rasha a Ukraine, tare da wasu da aka ɗauka ta hanyar yaudara, kamar yadda gwamnatin Ukraine ta bayyana cikin kwanankin bayan nan.