Iyayen ɗaliban Kuriga sun zaƙu su yi ido huɗu da 'ya'yansu

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY
Iyayen ɗaliban makarantar Kuriga da 'yan fashin daji suka sace ranar 7 ga watan Maris, sun ce sun zaƙu su yi ido huɗu da 'ya'yansu, bayan kuɓutar da su a ranar Lahadi.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gana da ɗaliban cikin daren Lahadi a wani wuri da ba a bayyana ba, inda ya tabbatar da cewa nan gaba a yau Litinin za a damƙa masa su a hukumance.
Rundunar sojin Najeriya ta ce an kuɓutar da daliban ne a cikin jihar Zamfara mai maƙwabtaka.
Da safiyar Lahadi ne, hukumomin suka sanar da rahoton kuɓutar da ɗaliban fiye da mako biyu bayan wasu 'yan bindiga sun sace su daga makarantarsu da ke garin Kuriga.
Wani bidiyo da gwamnan Kaduna, ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna ɗaliban zazzaune a kan tebura sanye da tufafin makaranta, kusan dukkansu sun yi buɗu-buɗu da kura, a bangare ɗaya kuma ga sojoji da Gwamna Uba Sani tsaye a gabansu suna jawabi.
Hukumomin sun ce ɗaliban da aka sace, su 137 ne, sai malaminsu guda daya, wanda ya riga mu gidan gaskiya, a lokacin da suke tsare a hannun 'yan bindiga.
Rahotanni sun ce tun farko, gwamnatin jihar Kaduna ta tsara damƙa ɗaliban hannun iyayensu ne a ranar Lahadi, sai dai bayan shafe tsawon sa'o'i suna zaman jira, ga dukkan alamu hakan ba ta samu ba.
Ya shiga cikin daliban da ke zazzaune a kan tebura, inda ya riƙa tambayarsu sunaye da azuzuwansu, tare da yadda suka kasance lokacin da suke tsare a hannun 'yan fashin daji.
Wani uban ɗaya daga cikin daliban, ya shaida mana cewa tuni hukumomi suka kira su zuwa gidan gwamnati, inda suke fatan yin ido hudu da 'ya'yansu.
Tun da farko, gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa bayan an damƙa wa gwamnatin Kaduna daliban za a shirya musu liyafa da yamma a Gidan Sir Kashim Ibrahim.
Shi ma wani uban ɗaya daga cikin ɗaliban da mu ka zanta da shi ta waya, ya shaida mana cewa sun zaƙu su ga 'ya'yan nasu.
Daga bisani, an zabi wasu daga cikin iyayen wadanda suka je suka gana da daliban, amma dai hukumomi sun shaida musu cewa sai washegari ranar Talata ne za a mika musu 'ya'yan nasu.













