Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana dambarwa tsakanin Kotun Ƙolin Brazil da Elon Musk
Wani alƙalin Kotun kolin Brazil ya umarci a gudanar da bincike kan mai kamfanin shafin X, wato Twitter a da, Elon Musk, inda ya zarge attajirin da kawo tarnaki ga ɓangaren shari'a.
Alkalin ya bayar da umarnin ne bayan da Mista Musk ya ƙi bin umarnin kotun tun da farko na rufe wasu shafuka, da ake gani na magoya bayan tsohon shugaban kasar ne, wadanda kotun ke ganin suna yada labaran karya da haifar da gaba.
Elon Musk wanda ya lashi takobin bijire wa umarnin mai shari’a Alexandre de Moraes, ya zargi alkalin da saba wa kundin tsarin mulkin Brazil da ma alummar kasar, a sau da dama.
A wani sako da ya sanya a shafinsa na X, mai kamfanin, ya ce alkali Moraes, ya umarci shafin X, da ya toshe shafukan wasu daidaikun mutane, da suka sanya wasu bayanai da ake ganin sun saba da tsarin dumukuradiyya.
Da yawa daga cikinsu na magoya bayan tsohon shugaban kasar ne, mai ra’ayin rikau, Jair Bolsonaro, wanda ya kira Elon Musk "a matsayin gwarzon gaske na dumukuradiyyar Brazil.
Mista Musk ya ce alkalin ya yi barazanar cin kamfanin tara, tare da barazanar kama ma’aikatansa, wanda hakan ke zama wata barazana ga wanzuwar kamfain a kasar mafi girma a Latin Amurka.
Da farko dai shafin na X ya bi uamrnin, wanda yana daga wani babban mataki a kasar ta Brazil na rufe shafukan sada zumunta d muhawara na mutane, wadanda ake ganin suna yada bayanai na karya da yada kiyayya.
To amma kuma daga baya Elon Musk wanda ya mallaki shafin tun 2022, ya fada a wasu sakonni da ya rinka sanyawa a jere a jere cewa za a dawo da dukkanin wadannan shafukan da aka rufe.
Bugu da kari Mista Musk wanda ya lashi takobin kalubalantar umarnin a kotu, ya ma ce ba ma sake bude fitattun shafukan mutanen, wadanda ba a bayyana sunayensu ba, zai ma wallafa cikakken umarnin alkalin, duk da cewa mai shari’ar ya hana yin hakan.
Babban mai tattara kararrai na kasar ta Brazil, Jorge Messias, ya soki matakin na Mista Musk, tare da yin kira da a kara daukar matakai na sa ido da takaita ayyukna shafukan sada zumunta da muhawara domin abin da ya kira hana kafofin kasashen waje keta dokokin Brazil.
Ya ce ba za su lamunta da yadda wasu hamshakan attajirai da ke zaune a kasashen waje ba, za su kasance da iko a kan kafofin sadarwa su kuma sanya kansu a matsayin saba wa doka, da kuma kin bin umarnin kotun kasar ba har ma da barazana ga hukumomin kasar ba.
Alkali Moraes, wanda shi ne ke jagorantar binciken da ake yi wa tsohon shugaban kasar na zargin yunkurin juyin mulki, yana daya daga cikin alkalan kotun kolin, da ke nuna ba sani ba sabo wajen yaki da baza labaran karya a Brazil.