Me ya sa gaba tsakanin Davido da Wizkid ta ƙi ci ta ƙi cinyewa?

Wizkid da Davido, biyu daga cikin jiga-jigan mawaƙan Najeriya sun mamaye zantuka a shafukan sada zumunta bayan da cacar-baki ta kaure a tsakanin su.

Manyan mawaƙan biyu na da miliyoyin mabiya a faɗin duniya kuma dama an daɗe ana kallon su a matsayin waɗanda ba su ga-maciji da juna.

Yawancin masu son waƙoƙin Najeriya na alaƙanta kansu da ko dai goyon bayan Davido ko kuma Wizkid.

A ranar Litinin da daddare ne cacar-baki ta kaure tsakanin manyan mawaƙan bayan da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta suka buƙaci Wizkid ya saki sabuwar waƙa.

Daga nan ne Wizkid ya mayar da martani ta hanyar wallafa wani bidiyon da aka riƙa yaɗawa a baya, inda a cikin bidiyon aka nuna wani mutum ya durƙusa ya na neman alfarma daga wurin wani da ba a san ko wane ne ba.

Wizkid ya ce idan masoyansa za su iya roƙon shi kamar yadda mutumin ke roƙo a cikin bidiyon, to zai saki sabuwar waƙa.

A baya masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi zargin cewa Davido ne mutumin da aka gani ya na roƙon alfarma a cikin bidiyon, sai dai Davido ɗin bai ce komai ba game da wannan zargi.

Da yammacin ranar Litinin ne Davido ya mayar wa Wizkid martani, inda ya ce ba zai "ɓata lokacinsa" kan "wani wanda tauraruwarsa ta dusashe bayan an yi ƙoƙarin farfado da ita a ƴan shekarun da suka gabata ba".

Wannan lamari ya sanya mutane na ta tofa albarcin baki a shafukan sada zumunta da kuma a fili.

Yanzu haka dai magoya bayan mawaƙan biyu na ci gaba da musayar kalamai domin kare gwarazan nasu.

Ana ganin cewa dai Daido da Wizkid su ne mawaƙa biyu mafiya shahara a nahiyar Afirka.

Dukkanin su sun lashe lambobin yabo na bajinta a ɓangaren waƙa kuma sun yi haɗaka da shahararrun mawaƙan duniya kamar Drake da Chris Brown da Nicki Minaj.