George Weah na neman ƙarin lokaci duk da fitintinun da ke damun Liberia

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Azeezat Olaoluwa da Yūsuf Akínpẹ̀lú
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Daga birnin Monrovia
Tsohon tauraron ƙwallon ƙafa George Weah yana takarar neman wa'adi na biyu tsawon wata shekara shida a matsayin shugaban ƙasar Laberiya.
Sai dai ga alama, ya yi wa kansa illa saboda ya gaza sauraron batun da ya mamaye kafofin yaɗa labarai da kan tituna - a kan buƙatar neman kafa kotun hukunta laifukan tattalin arziƙi da kuma na yaƙi.
Ɗan siyasar mai shekara 57 ya hau kan mulki ne da alƙawarin samar da ayyuka da kawu sauyin rayuwa da kafa kotun. Sai dai bayan ɗarewa kan mulki a 2018, ya musun cewa komawa baya kan tsoffin laifukan da aka aikata, ba hanya ce mafi alheri ga muradin ci gaban ƙasa ba.
Lamarin da wani matashi Frederick Tulay ɗan shekara 24, yake jin kuskure ne.
"A matsayina na mai zaɓe karon farko a 2017, ina da imani a kan Shugaba Weah. Sai dai ya ƙi magance matsalar cin hanci da ta yi katutu a cikin harkar aikin gwamnati.
Matasa da yawa sun auka shan ƙwaya saboda ba su da aikin yi," kamar yadda ya faɗa wa BBC, yana cewa a wannan karo ba zai zaɓi Weah da jam'iyyarsa ta CDC ba.

Asalin hoton, FREDERICK TULAY
Frederick Tulay ya rasa aiki a wani kamfanin gine-gine tsawon shekara biyu da ta wuce, lokacin da tsohon maigidansa ya kasa ci gaba da biyan albashinsa.
Yana aiki ne yanzu a matsayin ɗan taksi amma harkar ba ta garawa: "Tituna sun yi matuƙar lalacewa kuma iskar gas ta yi tsada sosai. Burina shi ne na bar ƙasar nan."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kalamansa yana nuni ne da fushin da ya zama ruwan dare - na cewa shekara 20 bayan kawo ƙarshen miyagun yaƙe-yaƙen basasar ƙasar biyu, waɗanda aka ƙiyasta cewa kimanin mutum 250,000 sun halaka, mafi yawan mutane har yanzu na faɗi-tashi kan yadda za su rayu.
Ƙasar tana aiki da wani tsarin kuɗi guda biyu, abin da ke nufin waɗanda aka biya kuɗi da dalar Laberiya sau tari suna buƙatar sayen abinci da sauran kayan masarufi da ake shigarwa ƙasar da dalar Amurka -lamarin da ya sa rayuwa ta yi matsananciyar tsada.
Badaƙalolin kuɗi guda biyu da suka faru a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan sun firgita al'ummar Laberiya, abin da ya janyo har Amurka ta ƙaƙaba takunkumai a kan jami'an gwamnati da dama ciki har da shugaban ma'aikatan George Weah.
Ga Peterson Sonyah mai shekara 49, gaza maganin raunukan da aka ji a baya ne, ta haddasa wannan al'ada ta aikata laifi cikin galatsi.
Mutumin wanda ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan kisan ƙare dangi lokacin yaƙin basasa a wani coci da ke babban birnin Monrovia, a yanzu yana amfani da lokacinsa wajen gangamin cewa mutanen da suka tafka aika-aika a yaƙe-yaƙen basasar, da kuma waɗanda suka ci gajiyar samun riba daga yaƙe-yaƙen, an gurfanar da su gaban kotu.
Lokacin yana ɗan shekara 16, matashin ya nemi mafaka a cocin tare da mahaifinsa, wanda yana ɗaya daga cikin kimanin mutum 600 da sojoji suka hallaka a 1990.
"Sa'ar da harsasan sojoji suka ƙare, sai wasu suka fita don samo ƙari, don haka mutane suka yi ƙoƙarin kuɓuta amma sai sojoji suka auka musu da adduna suka yi sara," yana tunawa, lokacin da yake nuna hudojin da harsasai suka yi wa tagogin Cocin St Peter ta Lutheran.

Asalin hoton, BBC/GIFT UFUOMA
Buƙatar kafa kotu, buƙata ce da ake da ita ta gaggawa, ya nanata: "Wasu mutane tun tuni suke faɗa min cewa tun da babu shari'ar adalci, kamata ya yi mu ɗauki makamai, mu ƙaddamar da yaƙi a kan mutanen.
"Sun yi imani idan muka yi haka, a gaba za mu samu ayyuka masu maiƙo kuma za mu yi rayuwa mafi inganci saboda suna ganin misali. Dukkanmu 'yan adam ne, kuma zuciya ba ta da ƙashi."
Cikin 'yan takara goma sha tara da ke ƙalubalantar George Weah a zaɓen shugaban ƙasa na ranar Talata mai zuwa, har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Joseph Boakai da ɗan kasuwa Alexander Cummings da kuma lauyan kare haƙƙin ɗan'adam Tiawan Gongloe.
Waɗannan 'yan takarar uku sun yi alƙawarin kafa kotu, idan an zaɓe su - ko da yake, wasu suna bayyana tantama a kan alƙawarin Joseph Boakai, saboda ƙawancen da yake yi da tsohon jagoran yaƙi Prince Yormie Johnson, wanda a yanzu sanata ne mai ci.
Ɗaya daga cikin kiraye-kirayen neman a kafa kotu da aka fi jin amonsa, ya fito ne daga Yekeh Kolubah, wani tsohon sojan yarinta, wanda 'yan tawayen NPLF na Charles Taylor suka ɗauka aiki a shekarun 1990, kuma shi ɗan majalisar dokoki ne daga lardim Montserrado.
Ya na son duk waɗanda ake zargi sun tafka aika-aika, su gurfana a gaban kotu - ciki har da shi kansa.
"Mu na buƙatar kotun hukunta waɗanda aka samu da yiwa tattalin arziƙi zagon ƙasa, ni ma ina so in je don kotu ta wanke ni, zan so mutane su san laifin da na aikata don a yi min hukunci.''
Sojan yarintar mai farin jini tsakanin matasa wanda ya koma ɗan siyasa, ya zauna a wata kujerar roba cikin kwarjini irin na sojoji lokacin da zai amsa tambayoyin ƴan jarida a Monrovia.
Kamar Mista Sonyah, shi ma ya yi imanin Kotu za ta kawo karshen matsalar da ta addabi Liberia:
"Idan bamu ɗauki wannan mataki ba, to kamar mun goyi bayan yaƙi ne. Rashin hukunci ne ya sa mu ke yawan tashin hankali.
"Da na je gidan yari saboda cin zarafin mutane ko kashe su ku na ganin zan sake tunanin ɗaukar bindiga?''
Ya bayyana takaicin yadda wasu suke yunƙurin hana shi magana, ta hanyar yi masa tayin shiga kwamitin da zai samu kuɗaɗe a majalisa.
Ministan yaɗa labarai Ledgerhood Rennie ya shaidawa BBC cewar shugaban ƙasa ba zai ce komai ba game da waɗannan zarge-zarge, tare da bayyana Mista Kolubah a matsayin mai lalurar taɓin hankali".
Mataimakin Ministan Kuɗi ya ƙara da cewar hukuncin laifukan yaƙi alhaki ne da ya rataya a wuyan majalisa.

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar bincike ta (GJRP), wadda ta yi aikin tattara bayanan abubuwan da suka faru a ƙasar lokacin yaƙi, ta ce babu tabbas gwamnatin za ta yi abin da ake buƙata.
Shugaban ƙungiyar Mista Hassan Bility ya ƙara da cewar kashi 50 na ƴan majalisa da suka haɗa da Mista Kolubah sun buƙaci a tattauna batun a majalisa amma sau biyu kakakin majalisar ya na ƙin bayar da goyon baya ba.
Wannan shi ne karon farko da za a yi zaɓe bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya bayan kawo ƙarshen yaƙin basasa a hukumance a shekara ta 2003.
Mista Wolokolie ya ce shugaban ƙasar ya cancanci jinjina sakamakon yadda ya jagoranci ƙasar lokacin annobar korona da kuma samar da ayyukan yi.
Magoya bayansa ma sun yaba masa saboda gina hanyoyi a faɗin ƙasar cikin shekaru 6, ya taɓa cewar shi ne maganin da ake buƙata na gyaran hanyoyi dalilin da ya sa ƴan siyasa suke kiransa da sunan "Bad Road Medicine".
Tsohon ɗan kallon Fifa na shekarar ya na da farin jinin da har yanzu ya ke amfani da shi wajen tara jama'a a lokutan yaƙin neman zabe a babban birnin ƙasar.

Asalin hoton, MOSES GARZEAWU
Wleh Potee, mai goyon bayan shugaban ƙasar kuma mai sana'ar sayar da agogon hannu da tabarau a tsakiyar Monrovia, ya lura cewa taɓarɓarewar tattalin arziƙi ba ta durƙusar da Laberiya gaba-ɗaya ba.
Duk da cewar ciniki ya ragu amma ƴan kasuwa na ƙaunar shugaban.
"A baya ƴan sanda sun rika ƙwace mana kayanmu kuma mun kashe maƙudan kuɗaɗe don karɓo kayan. Amma a karkashin wannan gwamnatin ƴan sanda sun daina tsangwamarmu. Don haka mun samu kwanciyar hankali."
An kuma amince da samun ƴancin faɗin albarkar baki a gwamnatin Weah, kodayake Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa game da hare-haren da ake kaiwa ƴan jarida kafin zabe.
Dillalin agogon mai shekaru 46 wanda ya karanci ilimin Akanta ya bayyana goyon bayansa ga kaddamar da kotun, ya kuma ƙara da cewar ba don yaƙin ba da yanzu ya kammala karatun babban digiri:
"A kawo kotun da za ta rataye su gabaɗaya."
Mista Sonyah yana fatan duk wanda aka zaɓa shugaban kasa, zai saurari ra'ayoyin jama'a da ƴan majalisar dokoki tare da goyon bayan a hukunta lafukan da aka tafka a baya domin ci gaba da kuma kawo ƙarshen cin hanci a Liberia.
"Zaman lafiya ba tare da hukunci ba kamar shayi ne ba sikari," cewar Mista Sonyah.










