Ɗanjaridar Ghana Godwin Asediba ya lashe gasar BBC ta Komla Dumor 2025

Lokacin karatu: Minti 3

Ɗanjaridar Ghana, Godwin Asediba ya lashe gasar BBC ta Komla Dumor ta 2025.

Matashin ɗanjaridar mai bincike, kuma mai shirya fina-finai sannan mai gabatar da labarai, shi ne mutum na 10 da ya lashe gasar tarihi.

Mista Asediba na aiki da gidan talbijin na TV3 da wasu gidajen FM har uku a Ghana.

Labaransa sun bayyana a manyan kafofin yaɗa labarai na duniya.

Mai shekara 29 na mayar da hankali kan labaran da suka shafi rayuwar mutane da nufin neman adalci tare da fito da muryoyin al'umomi marasa rinjaye.

Gasar da a yanzu ke cika shekara 10, an ƙirƙireta ne da nufin karrama Dumor, ɗan jaridar Ghana mai gabatar da shirye-shirye a BBC, da ya mutu yana da shekara 41 a 2014.

Dumor ya yi aiki matuƙa ba tare da gajiya ba da nuna jajircewa da sadaukarwa domin kawo labarai kan nahiyar Afrika inda ya nuna ƙwazo da juriya.

"Tarihin Komla na tuna mana da cewa ya kamata a fito da labaran Afirka a faɗe su cikin zuzzurfan bincike da mutuntawa ba tare da fargaba ba,'' in ji Asediba.

''Lashe gasar ba nasara ce kaɗai gare ni da mutanen Ghana ba, har da ƙwarin gwiwa ga aikin jarida da faɗakar da mutane da sanar da su tare da sauya musu tunani'', in ji shi.

Alƙalan gasar sun ce aikin Asediba ya yi matuƙar ƙayatar da su, da kuma yadda ya ɗauki aikin jarida da mutuntawa.

Ɗaya daga cikin labari da yake alfahari da su, shi ne binciken da ya yi kan ɗaya daga cikin ɗakunan ajiyar gawarwakin Ghana da aka yi watsi da shi, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiyar mutane.

A nan gaba kaɗan ne Asediba zai je ofishin BBC da ke Landan, inda zai shafe watanni uku yana aiki da sashen labarai tsakanin radiyo da talbijin da kuma shafin intanet.

Haka kuma zai samu horon sanin makamar aiki daga manyan ƴan jaridar BBC.

"Cikin shekara 10 da suka gabata, gasar Komla Dumor ta taimaka wajen horon zaƙaƙuran ƴanjarida daga nahiyar Afirka. Abin alfahari ne yadda suke yin fice tare da aiwatar da abubuwa masu amfani a BBC da wajenta,'' a cewar daraktar Afirka ta BBC, Juliet Njeri.

"Cika shekara 10 da fara wannan gasa shaida ce mai ƙarfi ga ɗorewar tarihin Komla Dumor: sha'awarsa da jaruntarsa ga ingantattun labarai da kuma ɗaukaka muryoyin Afirka."

Daga cikin tanadin gasar, Asedibe zai je wata ƙasar Afirka domin bayar da rahoton da za a saka a babbar tashar BBC.

Mutanen da suka taɓa lashe gasar a baya sun haɗa da Rukia Bulle da Paa Kwesi Asare da Dingindaba Jonah Buyoya da Victoria Rubadiri da Solomon Serwanjja da Waihiga Mwaura da Amina Yuguda da Didi Akinyelure da kuma Nancy Kacungira, wadda ta fara lashe gasar.

A shekarar da ta gabata, Bulle ta je Senegal, domin yin wani rahoto kan wasu mabiya addinin muslunci da ke wata shiga ta musamman.